Gwamnonin APC Zasu Shiga Ganawar Sirri Da Buhari Kan Lamarin Naira Da Tsadar Mai

Gwamnonin APC Zasu Shiga Ganawar Sirri Da Buhari Kan Lamarin Naira Da Tsadar Mai

  • Gwamnonin jam'iyyar APC sun dira fadar shugaban kasa don zama ta musamman da Shugaba Buhari
  • Majiya ta bayyana cewa gwamnonin zasu yiwa Buhari magana game da lamarin karancin Najeriya
  • Har yanzu yan Najeriya na kwana a layin bankuna saboda karancin sabbin Naira bayan kwace tsaffi daga hannunsu

Abuja - Gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress APC zasu gana da shugaba Muhammadu Buhari game da zaben 2023, wahala da tsadar mai da kuma karancin takardun Naira.

Kwamitin kamfen Atiku/Shettima a jawabin da ya fitar a shafinsa na Tuwita ya bayyana cewa za'a yi wannan zama ne yau Juma'a, 3 ga watan Febrairu, 2023.

Gwamnonin zasu tattauna da Buhari ne kan lamarin wasu mutane a fadarsa da suke yiwa dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, zagon kasa.

Kara karanta wannan

Magana ta Fara Fitowa: El-Rufai Ya Yi Karin Haske Kan Manyan da ke Yakar Takarar Tinubu

APC govs
Gwamnonin APC Zasu Shiga Ganawar Sirri Da Buhari Kan Lamarin Naira Da Tsadar Mai Hoto: Aso Rock
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya tayar da kura ranar Laraba inda yace akwai wasu a fadar shugaban kasa dake yiwa jam'iyyar APC zagon kasa kada ta samu nasara a zaben 2023.

Yace ko kadan gwamnoni basu tare da wannan lamari na sauyin kudi kuma an yi ne kawai don a tsanantawa yan Najeriya kuma kada a zabi Tinubu.

El-Rufa'i ya goyi bayan Tinubu, Yace Lallai ana yi masa zagon kasa daga ofishin Buhari

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa'i ya bayyana cewa akwai wasu yan tsiraru a fadar shugaban kasa da basu son dan takaran shugaban kasan APC, Bola Tinubu, ya ci zaben bana.

El-Rufa'i ya bayyana hakan a shirin Sunrise Daily, na gidan talabijin Channels ranar Talata.

Duk da bai bayyana sunayen wadannan yan tsiraru ba, ya ce har yanzu suna jin haushi saboda wanda suke so ba shi yayi nasara a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC ba.

Kara karanta wannan

Da Gaske Buhari Ya So Ahmad Lawan Ya Maye Gurbinsa? El-Rufai Ya Warware Abun da Buhari Ya Fada Masu

Ya ce suna amfani da Shugaba Muhammadu Buhari wajen cimma manufofinsu.

Yace:

"Ina ganin akwai wasu yan tsiraru a fadar shugaban kasa da suke son mu fadi zaben nan saboda basu samu abinda suke so ba; suna da nasu dan takaran da suke so kuma bai yi nasara a zaben sharen fagge ba."
"Suna kokarin ganin mun fadi zabe, kuma suna amfani da shugaban kasa saboda yana son yin abinda ya dace."

Asali: Legit.ng

Online view pixel