Wike Ya Umurci Shugabannin Kananan Hukumomi Jiharsa Su Yiwa Tinubu Kamfe

Wike Ya Umurci Shugabannin Kananan Hukumomi Jiharsa Su Yiwa Tinubu Kamfe

  • Kwamitin kamfen Atiku/Okowa ta bankado wanda Gwamna Nyesom Wike zai goyi baya a zaben 2023
  • Wike ya hana kwamitin kamfen Atiku amfani da babban filin kwallo don taron yakin neman zabe
  • Saura kwanaki ashirin da uku (23) a gudanar da zaben shugaban kasa, sanatoci da yan majalisar wakilai

Rivers - Kwamitin yakin neman zabe na uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), shiyyar jihar Rivers ta bayyana dan takarar jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, matsayin zabin gwamna Nyesom Wike a zaben bana.

Kwamitin a wasika mai kwanan wata 1 ga Febrairu tace Wike tuni ya umurci dukkan shugabanni kananan hukumomin jihar, hadimansa, da shugabannin jam'iyya su yiwa Tinubu aiki, rahoton TheNation.

Wikey
Wike Ya Umurci Shugabannin Kananan Hukumomi Jiharsa Su Yiwa Tinubu Kamfe
Asali: Twitter

Wasikar da aka aikewa Wike kuma Diraktan kwamitin kamfen Atiku/Okowa, Abiye Sekibo, a matsayin martani kan dalilin soke izinin amfani da filin kwallon Adokiye Amiesimaka don yakin neman zaben Atiku.

Kara karanta wannan

Tinubu Gida-gida: Yadda Aka Gudanar Gangamin Tallata Tinubu Da Shettima Har Gida Ga Mazauna Wata Jahar Arewa

Sekibo ya tuhumci Wike da kokarin hana dan takararsu, Atiku Abubakar, daga kamfe a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa Wike yana yiwa jam'iyyar zagon kasa kuma yana hassada kan karbuwan da Atiku ya samu a jihar Rivers.

A cewarsa:

"Mun samu labarin cewa kai umurci dukkan shugabannin kananan hukumomi, masu baka shawara, kwamishanoni, shugabanni jam'iyya a matakin kananan hukumomi da gundumomi da dukkan wadanda ka baiwa mukami su yiwa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu aiki."
"Maganganun da kake yi a bainar jama'a, habaice-habaicen da kake yi duk sun nuna cewa kana kokarin ganin cewa dan takaran shugaban kasan PDP ba ci zabe ba."

Muna nan zaku gani Atiku ba zai lashe zaben 2023 ba, Wike

A wani labarin, gwamnan Rivers, Nyesom Wike ya sake fitowa ya caccaki dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyarsa PDP, Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Kaico: Atiku ya rasa babbar dama, shugaba a jihar su abokin takararsa ya ballo ruwa

Wike ya shiga takun saka da Atiku tun bayan zaben fidda gwanin yan takara da ya sha kashi.

Wike ya bayyana cewa sai ya yi duk mai yiwuwa don ganin cewa Atiku bai shaki kamshin kujerar shugaban kasa ba.

Gwamnan nan Rivers ya ce tun kan Atiku ya hau mulki ya fara musu barazana ina ga ya hau.

Ya ce zai koyawa uwar jam'iyyar PDP darasi.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel