Sai Na Tabbatar Atiku Ya Fadi Zabe Saboda Abinda Ya Min: Nyesom Wike

Sai Na Tabbatar Atiku Ya Fadi Zabe Saboda Abinda Ya Min: Nyesom Wike

  • Nyesom Wike ya sake fitowa ya caccaki dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyarsa PDP
  • Wike ya shiga takun saka da Atiku tun bayan zaben fidda gwanin yan takara da ya sha kashi
  • Gwamnan nan Rivers ya ce tun kan Atiku ya hau mulki ya fara musu barazana ina ga ya hau?

Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ana ta yi masa bita da kulli a cikin jam'iyyar PDP saboda yana adawa da Atiku Abubakar, dan takaran shugaban kasa.

Wike ya ce ana yi masa bita da kulli saboda kawai yana da'awar adalci cikin jam'iyyar kuma wannan abu zai kayar da jam'iyyar a zaben shugaban kasa.

Wike ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin taron kamfen a garin Mogho dake karamar hukumar Gokana dake jihar.

Kara karanta wannan

Bidiyon Matashi Hankali Tashe Yana Nadamar Son Kudinsa, Yace Kwanaki Kadan Suka Rage ya Mutu

Atiku
Sai Na Tabbatar Atiku Ya Fadi Zabe Saboda Abinda Ya Min: Nyesom Wike
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa barazanar da ake masa da tamkar ban dariya kuma masu yi masa barazana ba zasu taba nasara a zabe ba.

A cewarsa:

"Kun gani a YouTube yadda suke cewa zasu hukunta ni idan suka lashe zabe. Ba zaku yi nasara a zaben ba."
"Tun baku lashe zabe ba, kun fara barazanar cin mutuncin wasu mutane. Shin Ubangiji zai barku? Dukkansu na shiri suna cewa zasu ladabtar da su, basu isa ba, kuma idan sun isa su gwada."

Ya ce zaben 2023 na jama'a masu katin PVC ne, shine karfin mutane, kuma ba zai zama kamar zaben 2019 da akayi amfani da sojoji wajen baiwa jama'a tsoro ba.

Atiku Na So ‘Ya’yansa 31 Su Zamo Attajirai Kamar Shi Shiyasa Yake Son Zama Shugaban Kasa, Tsohon Hadiminsa

A wani labari kuma mai tashe, wani tsohon hadimin Atiku Abubakar wand aya saki faifan bidiyon da aka ji suna maganan yadda aka wawure kudin Najeriya, Michiel Achimugu, ya sake caccakan dan takaran.

Kara karanta wannan

Ya fasa kwai: Tinubu ya fadi makarkashin yin sabbin Naira da karancin mai a Najeriya

Achimugu ya fito tashar TVC ya bayyana cewa yan Najeriya suyi hattara a kan zabar tsohon maigidansa Atiku Abubakar a zabe mai zuwa, saboda ba mutumin kirki bane.

Yace manufar Atiku itace ya mutu ya bar 'yayansa sama da talatin su zama manyan masu kudi.

Ya ce yan Najeriya su duba yadda 'yayansa ke yi a jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel