Dattijo Ya Tubure, Ya Ce Ba Zai Karbi Tiransfa Ba a Kasuwar da Zai Siyar da Buhun Wakensa

Dattijo Ya Tubure, Ya Ce Ba Zai Karbi Tiransfa Ba a Kasuwar da Zai Siyar da Buhun Wakensa

  • Wani dattijo a kafar sada zumunta ya ba da dariya yayin da yace ba za a dauki buhun wakensa ba a yi masa tiransfa na kudi
  • Dattijon, wanda da alamu a kasuwar hatsi yake ya ce shi dai kudi dumus kawai za a bashi, matukar ana son siyan kasyansa
  • Jama’ar kafar sada zumunta sun yi martani mai daukar hankali bayan ganin bidiyon dattijon da aka yada a kafar Facebook

Wani dattijo dan Arewacin Najeriya ya turje tare da bayyana ba zai karbi kudi ta hanyar tiransfa ba, sai da a bashi a hannu.

Dattijon da ba a bayyana sunansa ba an ganshi a kasuwa yana dariya tare da nesanta bayyana ba zai siyar da buhun wakensa ba sai idan tsabar kudi za a bashi.

A bidiyon da Jaafar Jaafar ya yada a Facebook, an ji lokacin da wani mutum ke tambayar dattijon ko zai amince a tura masa kudi ta banki shi kuwa ya ba da kaya.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Bidiyon Tsohon da Yayi Shekaru 61 ba Bacci Kuma Yana Raye a Duniya

Dattijo ya cije, ya ce sai dai kudi a hannu
Dattijo Ya Tubure, Ya Ce Ba Zai Karbi Tiransfa Ba a Kasuwar da Zai Siyar da Buhun Wakensa | Hoto: Jaafar Jaafar
Asali: Facebook

Cikin dariya da raha, dattijon yace sam ba zai amince ba, shi dai ya ji musu kawai kafin a dauki kayansa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun yi raha da ganin wannan bidiyon, wasu sun ce basu ga laifinsa ba, domin a zamanin baya babu irin wannan tura kudi ta baki.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Ga kadan daga abin da mutane ke cewa:

Ibrahim Musa Gombe yace:

“Zaizo ya saba ai Bankin ma zuwan shi ba'a yarda dashi ba.”

Musa Muhammad Arewa yace:

“Tsoho yaji sanjin kudin buhari sau biyu kenan. 1984 chanjin kudi. 2022 chanji kudi. Baba Allah ya maka rahma.”

Ibrahim Ayuba yace:

“Jaafar Jaafar a ina ka samo bidiyon kasuwar hatsin Funtua?
“Dattawannan fa mahaifanmu ne aradu.”

Fadila H Aliyu tace:

“Tashin hankali, Baba bai yarda ya bayar da wake a ba shi lambobi ba.”

Kara karanta wannan

Bidiyo: Kare ya Firgita Bayan Yayi Ido 4 da Zaki, Ya Haidye Haushi da ya Fara don Tsoro

Lukman Ibrahim Barau yace:

‘Wallahi ba abun daria bane wannan. Najeriya bamu da wayewar da zamu daina amfani da kudi tsaba.”

Ibrahim G Musa Sheka yace:

“Shiyasa kuwa ai labari ya riskemu kayan abinci na ta sakkowa domin a samu kudi a hannu.”

Jikan Duduwa Funtua yace:

“Allah ya kawo Mana sauki Basu son transfer idan kana da kudi a hannu 13,000 masara”

Asali: Legit.ng

Online view pixel