Yadda Muryar Kare ta Disashe Bayan ya ga Zaki a Bidiyo ya Ba jama'a Mamaki

Yadda Muryar Kare ta Disashe Bayan ya ga Zaki a Bidiyo ya Ba jama'a Mamaki

  • Yadda wani kare yayi bayan hada idanu da zaki ya bar ma'abota amfani da soshiyal midiya cikin dariya da nishadi
  • Wani shafin Twitter mai suna @DailyLoud ya wallafa bidiyon mai bada dariya inda karen ya hdiye haushinsa a take
  • Jama'a sun kasa hakura, haka suka dinga yin dariya tare da kwasar nishadi kan wannan dabbar ta nuna karara

Karnika suna iya bibiyar maguna amma a bayyane za ka ga cewa karen ya fi karfin magen.

Wani ya fita da karensa inda ya nadi bidiyonsa bayan da yayi arangama da zaki. Hakan yasa aka gane cewa Zaki sarki ne ko a ina kuwa.

Karee ya ga Zaki
Yadda Muryar Kare ta Disashe Bayan ya ga Zaki a Bidiyo ya Ba jama'a Mamaki. Hoto daga Getty Images
Asali: Getty Images

Sau da yawa bidiyon dabbobi yana kasancewa mafi bada dariya a soshiyal midiya.

Dukkansu basu san abinda suke ba kuma lamurransu na iya baka dariya da sja'awa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: "Ba Zan Yarda Ba" Peter Obi Ya Maida Martani Mai Dumi Kan Nasarar Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

@DailyLoud da ake yawan bin shafin a Twitter suna wallafa wani bidiyo da ke nuna kare yana kin yi haushi bayan yayi arangama da zaki.

Abun mamakin shi ne, duk da ba muhallinsu daya ba, wannan karen ya san babbar magen nan ba tsararsa bace.

Kalla bidiyon:

"Karen ya san lokacin da bai dace yayi haushi ba"

'Yan soshiyal midiya sun kwashi nishadi kan abinda karen yayi

Jama'a sun kasa daurewa inda suka dinga dariya kan yadda karen ya kasa ko kwakwaran numfashi ballantana haushi mai karfi.

Sashin tsokaci ya cika dankam da jama'a inda suka dinga tofa albarkacin bakinsu.

@anthonyvclark20 yace:

"Wannan karen yayi guna-guni sannan haushin ya fito."

@im__Lexy tace:

“Ya rasa karen da ke jikinsa."

@williederrick3 yace:

“Ba ya son tada hazo."

@OpalWGG yace:

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben 2023: A Karshe Babban Sarkin Yarbawa Ya Magantu Kan Soke Zabe Da Obasanjo Ya Ce A Yi

“Haba yaro, ba za ka fatattaki wannan magen ba?"

@KayodeDamali yace:

“Wani yace karen yayi haushi da kanana baki kuma bai farfado ba har yanzu."

Miji ya ba matarsa kyautar adaidaita sahu biyu ranar bazday din ta

A wani labari na daban, wani miji nagari ya karfafa matarsa a fannin sana'a a maimakon kashe mata kudi a abinda zai sa ta dinga kashe kudi kullum.

A maimakon siya mata mota, ya siya mata adaidaita sahu biyu ranar murnar zagayowar haihuwarta.

Matar ta fashe da kukan farin ciki inda daga bisani ta tsaya ta dinga daukar hotuna da ababen sana'ar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel