Wata Mata da Danta Sun Lakadawa Surukinsu Na Jaki Har Rai Ya Yi Halinsa

Wata Mata da Danta Sun Lakadawa Surukinsu Na Jaki Har Rai Ya Yi Halinsa

  • Wata matar aure, Charity Upev, da ɗanta sun taru sun halaka surukinsu da duka kan ya saci nama a tukunya
  • Hukumar 'yan sanda ta kama waɗanda ake zargin kuma ta gurfanar da su a gaban Kotun Majistire dake Makurdi, jihar Benuwai
  • Bayan jin duk abinda ya faru daga bakin ɗan sanda mai shigar da kara, Kotu ta ɗage zaman shari'ar zuwa ranar 8 ga watan Fabrairu

Makurdi, Benue - Wata Kotun Majistire mai zama a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai ta umarci a garkame wata mata da ɗanta a magarkama kan zargin kisan kai.

Punch tace Kotu ta aika da matar yar shekara 40 a duniya msi suna, Charity Upev, tare ɗan da ta haifa, Tertsea, bisa zargin da ake masu na ajalin surukinsu.

Alamar Kotu.
Wata Mata da Danta Sun Lakadawa Surukinsu Na Jaki Har Rai Ya Yi Halinsa Hoto: Punchng
Asali: Twitter

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa hukumar 'yan sanda ta kai Charity da ɗanta gaban Kuliya ne kan zargi biyu, haɗa baki da kuma kisan kai.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare, Gwamna Wike Ya Magantu Kan Ɗan Takarar Shugaban Kasa Da Zai Marawa Baya a 2023

Yayin zaman shari'ar, Alkalin Kotun mai shari'a Roseline Iyorshe, ba ta karɓi uzurin wadanda ake ƙara ba ta umarci a ci gaba da tsare su. Ta kuma ɗage zaman zuwa 8 ga watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda matar da ɗanta suka kashe suruki

Tun da farko mai gabatar da ƙara, Insufekta Jonah Uletu, ya shaida wa Kotu cewa a ranar 24 ga watan Janairu, DPO na Caji Ofis ɗin E dake Makurdi ya samu labarin matar da ɗanta sun lakada wa wani mai suna Fanen dukan tsiya.

Fanen, wani surukin matar ne dake zama a gida ɗaya da su. Mai ƙara ya ci gaba da cewa Charity ta yi ikirarin cewa Fanen ya ɗaukar mata nama daga tukunyar miya.

Insufektan ya ƙara da gaya wa Kotu cewa sakamakon wannan duka ne Fanen ya jigata ainun, nan da nan aka garzayi da shi Asibiti, amma rai ya yi halinsa ana tsaka da masa magani.

Kara karanta wannan

"Kunnen Ƙashi Gareta" Magidanci Ya Roki Kotu Ta Raba Aurensa Saboda Matar Tana Take Masa Hakki

A cewar ɗan sandan, wannan ɗanyen aiki da suka aikata ya saba wa sashi na 97 da 222 na kundin dokokim Fanal Kod, jihar Benuwai 2004, kamar yadda Lindaekeji ta rahoto.

A wani labarin kuma Magidanci ya Garzaya Kotu, Ya Nemi a Raba Aurensa Saboda matar Bata Masa Biyayya

Taiwo Ajadi, ya kai ƙarar matarsa gaban Kotun yanki a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, inda ya nemi a rasa aurensu kuma a ba shi 'ya'yansa.

Matar mai suna Mariam bata masa musu ba, ta amince da raba auren amma ba kan tuhumar da yake mata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel