Shugabancin Kasa: Manyan Yan Najeriya 3 Da Ba Su Son A Yi Zaben 2023 Da Dalilinsu

Shugabancin Kasa: Manyan Yan Najeriya 3 Da Ba Su Son A Yi Zaben 2023 Da Dalilinsu

  • Wasu fitaccen yan Najeriya har yanzu ba su ga dalilin da zai saka a yi zaben 2023 da ke tafe ba ba tare da sauya fasalin kasar
  • Irinsu Afe Babalola da Primate Ayodele suna cikin wadanda ke kira da cewa a yi wa kundin tsarin kasar garambawul
  • Babalola, a baya-bayan nan ya nuna cewa baya tsammanin zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu zai samar da shugabanni na gari da za su kawo irin canjin da ake so a kasar sai an sauya tsarin rabon arzikin kasar

A yayin da yan Najeriya ke shirin sauya abin da zai faru da kasarsu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, wasu manyan kasar sun yi kira da cewa a samar da gwamnatin wucin gadi suna mai cewa Najeriya bata bukatar zabe a yanzu.

Kara karanta wannan

Wahalar Naira Da Mai: Akwai Wasu Na Kusa Da Buhari Da Basu Son Tinubu Yaci Zabe, El-Rufa'i

Masu sukar zaben sun ce abin da Najeriya ke bukata a yanzu shine garambawul din kundin tsarin mulki da zai bawa dukkan yan Najerya hakinsu.

Okotie, Babalola
Shugabancin Kasa: Manyan Yan Najeriya 3 Da Ba Su Son A Yi Zaben 2023 Da Dalilinsu. Hoto: Photo Credit: Afe Babalola, Primate Ayodele
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duk da cewa majalisar tarayya tana yin wasu gyare-gyare ga kundin tsarin mulkin, kawo yanzu ba a magance mafi yawancin abubuwan da wasu yan kasar ke nema a musu ba.

Wasu daga cikin batutuwan da yan Najeriya ke son a gyara a kundin tsarin mulkin sun hada da yan sandan jihohi, bawa jihohi damar kula da albarkatunsu, ballewa daga kasar da sauransu.

Wasu manyan yan Najeriya 3 da suka yi kira da cewa a dakatar da yin zaben sune:

Afe Babalola

Kwararren lauya kuma malami ya dade yana kira da cewa a yi sabon kudin tsarin mulki a kasar, yana mai cewa sabon kudin mulki kasar ke bukata ba zabe ba.

Kara karanta wannan

Buhari ga ‘Yan Najeriya: Ku Dinga Godiya ga Allah, Sai Kun je Kasashe Masu Makwabtaka Zaku san Kuna Cikin Rahama

Tunda farkon wannan shekarar, dattijon ya dage cewa zaben da za a yi ba zai kawo wani sabbin canji ba idan ba a canja kundin tsarin mulkin ba.

Primate Elijah Ayodele

Primate Elijah Ayodele yana cikin manyan yan Najeriya da ke da mabiya sosai kuma shugaban na cocin INRI Evangelical Spiritual Church, a baya-bayan nan ya gargadi INEC ta dage zaben.

Yayin da ya ke kira ga INEC ta dage zaben saboda gudun sakamako wanda bai kammalu ba wato 'Inconclusive', malamin addinin ya ce sauya tsarin rabon arzikin kasar ya kamata a yi ba zabe ba.

Chris Okotie

Okotie fitaccen fasto ne a Najeriya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa shima ya dade yana kira a yi gwamnatin wucin gadi tun 2019 a maimakon babban zaben 2023.

A cewar malamin addinin, yayin da ya ke kara kira ga sauya tsarin rabon arzikin, ya ce Najeriya na bukatar gwamnati mai tsayuwa da kanta da siyasa mai nagarta wanda babu shi a yanzu.

Kara karanta wannan

Babu Gwamnati da Zata Iya Shawo kan Dukkan Kalubalen Najeriya ita Daya, Shugaba Buhari

A cewar Okotie, wadannan abu ne masu muhimmanci da ake bukata a kasar idan ana son cin nasara bayan 2023.

Ahmad Lawan ya bayyana muhimmin abu 1 da zai biyo bayan zaben 2023

Kun ji cewa a yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2023, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ce ya yi imanin hukumar INEC za ta yi zabe mai kyawu da sahihanci.

Lawan ya ce yana kyautata zaton zai zama mafi kyawu a tarihin Najeriya saboda gyaran dokar zabe da suka yi a majalisa da bullo da na'urar BVAS da ake sa ran za ta dakile magudin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel