Shugaban Majalisa Ya Bayyana Wani Muhimmin Abu 1 Da Zai Faru Bayan Zaben 2023

Shugaban Majalisa Ya Bayyana Wani Muhimmin Abu 1 Da Zai Faru Bayan Zaben 2023

  • Gabanin babban zaben shekarar 2023, shugaban majalisar dattawan Najeriya ya bayyana cewa ya yarda da hukumar zabe mai zaman kanta INEC
  • Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ce yana sa ran sahihin babban zabe a watanni masu zuwa
  • Ya kara da cewa sabuwar fasaha na zamani za ta sa zaben ya zama mafi nagarta da sahihanci a tarihin Najeriya

FCT, Abuja - Kasa da makonni hudu kafin fara babban zaben shekarar 2023, Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya bugi kirji ya ce zaben zai zama mafi kyawu a shekaru masu zuwa.

Ya yi wannan jawabin ne a Abuja ranar Talata, 31 ga watan Janairu yayin da ya karbi bakuncin tawagar Kungiyar Hadin Kan Turai (EU) karkashin jagorancin Thomas Boserup, mataimakin mai sa ido kan zabe.

Kara karanta wannan

Zamu Tabbatar Da Kun Samu Isasshen Mai Lokacin Zabe: NNPC Ya T

Ahmad Lawan
Shugaban Majalisa Ya Bayyana Wani Muhimmin Abu 1 Da Zai Faru Bayan Zaben 2023. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda The Cable ta rahoto, Lawan ya bayyana cewa majalisa ta taka rawa wurin shirin zaben da sabuwar dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima.

Hakazalika, Sanata Lawan wanda ke cike da kwarin gwiwa ya ce bullo da amfani da na'urar BVAS zai zama babban lamari da zai taimaka wurin dakile magudin zabe.

Ya ce:

"Ba mamaki babban zaben zai zama mafi kyawu. Domin mu a majalisa munyi aiki tukuru don samar da takarda mai muhimmanci da zai jagoranci zabe a Najeriya.
"Abin da ke karfafa mana gwiwa shine irin abin da muka bawa INEC. Ina tunain INEC hukuma ce mai muhimmanci. Shi yasa muke bata fifiko."

Zaben 2023: Majalisa na sa ran INEC za ta yi abin da ya dace - Sanata Lawan

Sanata Lawan kuma ya ce yana fatan INEC a matsayinta na hukumar zabe za ta yi abin da ya dace a zaben da ke tafe cikin ya makonni.

Kara karanta wannan

Sabon Salo: An Hana Mutane Marasa Katin Zabe Shiga Fadar Babban Sarki A Najeriya

Ya yi kira ga INEC ta bawa marada kunya yayin zaben na 2023.

Sanata Lawan ya ce bullo da BVAS ya riga ya warware wasu matsalar yiwuwar magudin zabe.

Ya ce:

"Muna son zaben 2023 ya zama sahihi kuma da gabatar da BVAS muna fatan za a samu hakan."

Sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 zai bawa yan Najeriya mamaki, Kwankwaso

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP ya ce sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 zai bawa yan Najeriya mamaki.

Kwankwaso ya bayyana kwarin gwiwa cewa shine zai lashe zaben shugaban kasa a zaben da ke tafe a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Tsohon gwamnan na Kano ya kuma musanta cewa yana shirin yin maja da dan takarar jam'iyyar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel