An Cafke Wani Tsohon Mai Laifi Dauke Da Bindigu Da Layyu A Taron Kamfen Din APC A Kwara

An Cafke Wani Tsohon Mai Laifi Dauke Da Bindigu Da Layyu A Taron Kamfen Din APC A Kwara

  • Wani dan kungiyar asiri da bai dade da fitowa daga gidan gyaran hali ba ya sake fadawa komar yan sanda
  • Mutumin mai shekaru 44 da aka kama a wurin taron APC da bindigu biyu ya kasa bayyana dalilin zuwan sa taron
  • Hukumar yan sandan Jihar Kwara ta bayyana cewa za ta mika shi gaban kotu da zarar an kammala bincike

Kwara - Rundunar yan sandan Jihar Kwara tace ta kama wani mutum mai shekara 44 ranar Lahadi a wajen taron yakin neman zaben APC a Ilorin, da bindigun gargajiya biyu da kuma layoyi, rahoton The Punch.

Yan sandan sun bayyana sunan mutumin mai matsakaitan shekaru Safi Abolaji da aka fi sani da Ojulari, wanda aka kama a wajen taron APC a Ojuekun Sarumi dake karamar hukumar Ilorin ta Yamma da ke Jihar kwara da tsakar ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Buhari a Kano: Jam'ian tsaro sun cika lungu da sako domin tarbar Buhari a yau Litinin

APC Logo
An Cafke Wani Tsohon Mai Laifi Dauke Da Bindigu Da Layyu A Taron Kamfen Din APC A Kwara. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rundunar yan sandan Jihar a wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar yan sandan Jihar, SP Ajayi Okasanmi, tace Abolaji dake a yankin Kankatu, Ilorin, an kama shi a wajen taron da wasu kananan bindigu da harsashi da kuma wasu layoyi.

Yace a binciken da suka gudanar sun gano wanda ake zargin tsohon da kungiyar asiri ne kuma tsohon mai laifi ne da bai dade da fitowa daga gidan yari ba.

Okasanmi ya ce:

''Muna ci gaba da bincike, kan lamarin da ya faru a taron yakin neman zaben APC da aka gudanar 29 ga Janairu, 2023, da misalin 3:30 na rana, da ya gudana a Ojuekun Sarumi, Ilorin, an kama wani Safi Abolaji aka Ojulari, namiji, mai shekaru 44 dake zaune a Kankatu, Ilorin, da taimakon al'ummar gari da kuma jami'an yan sanda da kananan bindigu dauke da harsashi da kuma laya.

Kara karanta wannan

Amarya Ta Antayawa Uwarginta Tafasashen Ruwa Kan Zargin Maita A Jihar Kwara

''Yayin bincike, wanda ake zargin wanda ya tabbatar da cewa a yanzu haka dan kungiyar asiri ne ta Aye, wanda kuma ba a dade da sallamar shi daga gidan gyaran hali ba bayan kammala wa'adinsa, ya kasa bayyana takamaiman dalilin da ya kaishi wajen taron, inda ya tabbatar da cewa shi dan jam'iyyar PDP ne a Jihar.
''Ana ci gaba da fadada bincike don sanin hakikanin manufarsa da kuma kama sauran yan kungiyar asirin tasu."

Ya cigaba da cewa:

''Kwamishinan yan sandan Jihar Kwara, CP Paul Odama, ya gargadi masu laifi a lokuta da dama da su tuba ko kuma su bar Jihar Kwara, saboda hukumar bazata lamunci duk abin da zai kawowa jihar koma baya ba a dukkan al'amura.''

Okasanmi yace za su mika wanda ake zargi kotu da zarar an kammala bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel