Jami’an Tsaro Sun Mamaye Ko’ina Yayin da Buhari Zai Kai Ziyara Kano

Jami’an Tsaro Sun Mamaye Ko’ina Yayin da Buhari Zai Kai Ziyara Kano

  • Jami'an tsaro sun mamaye jihar Kano yayin da suke jiran isowar shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • A yau 30 ga watan Janairu Buhari zai kai ziyara Kano don kaddamar da wasu manyan ayyukan da ya yi
  • A kwanakin baya Buhari ya kai ziyara jihar Katsina, inda ya kaddamar da wasu ayyuka a jihar da ke makwabtaka da Kano

Jihar Kano - An girke jami’an tsaro a yankuna daban-daban na jihar Kaduna a ranar Litinin gabanin isowar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ana tsammanin isowar shugaba Buhari jihar Kano ne domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatinsa ta yi, PM News ta ruwaito.

Da sanyin safiya da misalin karfe 7, an ga ‘yan sanda, jami’an NSCDC, KAROTA da na kiyaye hadurra a jibge a kwaryar birnin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ganduje ya Bayyanawa Buhari Matsayar Kanawa Kan Ziyarar da Zai Kai Jihar

Jami'an tsaro sun mamaye Kano
Jami’an Tsaro Sun Mamaye Ko’ina Yayin da Buhari Zai Kai Ziyara Kano | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Hanyoyin da jami’an tsaro suka mamaye sun hada na da Sabo Bakin Zuwo, wacce aka fi sani da hanyar gidan sarki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A tun farko, kwamishinan yada labarai na gwamnatin jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya ce an shirya komai domin tarbar shugaban kasan.

Abin da Buhari zai yi a Kano

A ziyararsa ta Kano, Buhari zai kaddamar da aikin wutar lantarki ta hasken rana mai yawan megawat 10 da gwamnatinsa ta yi a Kano da ake kira da Kano Grid Solar Power.

Hakazalika, da aikin tashar cikin gida mai darajar biliyoyi da aka sanyawa Dala Dry Port da ke Zawachiki a karamar hukumar Kumbotso.

Haka nan, zai kaddamar da Data Center na da ke a sakateriyar Audu Bako, da dai sauran ayyuka masu alaka da hakan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Duk Da Rashin Amincewar Ganduje, Buhari Zai Kai Ziyara Jihar Kano a Gobe Litinin

Sauran ayyukan da za a kaddamar sun hada da asibiti, wurin koyar da sana’a da kuma jerangiyar gidaje da aka gina da dai sauransu.

Akwai jami'an tsaro, ga cunkoso amma babu hantara

Majiya daga jihar ta Kano ta shaidawa Legit.ng Hausa cewa, jami'an tsaron na yin abin da ke gabansu ne, mutane ma haka.

Babu alamar hargitsi ko tashin hankali daga mutanen Kano, haka nan babu alamar hantara daga jami'an tsaron.

Idan baku manta ba, ziyarar Buhari a jihar Katsina ta zo da tsaiko, domin matasa sun barke da zanga-zanga a jihar lokacin da shugaban ke zagayawa a jihar.

Wannan tarzoma da ta tashi ta kai ga 'yan sanda suka kama wasu mutane takwas da ake zargi suna da hannu a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel