Muna da Isassun Sabbin Takardun Kudi a Wurinmu, CBN Ya Jaddada

Muna da Isassun Sabbin Takardun Kudi a Wurinmu, CBN Ya Jaddada

  • CBN ya kara jaddada kalamansa na baya cewa akwai isassun sabbin kuɗin da aka bugo ta yadda Yan Najeriya ba zasu wahala ba
  • Jami'ar babban bankin, Lydia Alfa, ce ta faɗi haka yayin da ta fita yawon sanya ido kan yadda sabon tsarin ke tafiya a Yola
  • Ta shawarci yan Najeriya su yi amfani da karin wa'adin nan wurin musanya kuɗinsu kar su jira sai lokaci ya kure

Adamawa - Babban bankin Najeriya (CBN) ya jaddada cewa akwai isassun takardun sabbin kuɗin da aka canja domin 'yan Najeriya.

The Nation ta ruwaito cewa ma'aikatan CBN ne suka yi wannan ikirarin yayin da suke yawon duba yanayin yadda kuɗin ke zuwa hannun jama'a a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Takardun naira.
Muna da Isassun Sabbin Takardun Kudi a Wurinmu, CBN Ya Jaddada Hoto: thenationonline
Asali: Getty Images

A cewar babban bankin, abu ɗaya da bankuna zasu yi a basu kuɗin nan take shi ne su tura bukatar sabbin kudi ga CBN.

Kara karanta wannan

An Samu Cigaba: CBN Ya Fitar da Sabuwar Sanarwa Ga Masu Cire Sabbin Kudi a ATM

Daraktan sashin bincike na cikin gida a CBN, Lydia Alfa, ta yi kira ga 'yan Najeriya kar su daga hankulansu kan rashin sabbin kuɗin musamman a yanzu da aka kara wa'adin musaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kuma shawarci 'yan Najeriya kar su yi jinkiri ganin cewa akwai sauran lokaci kafin 10 ga watan Fabrairu su yi duk me yuwuwa su tabbatar sun ba da tsoho an musanya masu da sabon kuɗi.

Lydia Alfa ta ƙara da cewa tuni suka umarci bankunan kasuwanci su zo su karɓi duk iya yawan kudin da suke buƙata kuma su tabbata wakilansu sun samu isassu domin sabbin kudin su isa hannun jama'a.

Haka zalika ta ce na daga cikin dalilansu na ganawa da 'yan Najeriya daga tushe a faɗa masu cewa CBN ya kara wa'adin musanyar kuɗin da kuma gargaɗinsu da su guji nuna wariya.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama ainihin mutanen da ke boye sabbin kudi, suna siyarwa a boye a Arewa

"Bai kamata mu tsaya mu koma gida mu kwanta ba saboda nan gaba mu dawo cikin gaggawa bayan mun riga mun salwantar da lokaci mai muhimmanci," inji ta, kamar yadda Punch ta ruwaito.

CBN Ya Fitar da Sabuwar Sanarwa Ga Masu Cire Sabbin Kudi a ATM

A wani labarin kuma Babban banki CBN Yace Yana Raba Wa Bankuna Miliyan N30m Na Sabbin Naira a Kowace Rana

Babban Bankin Najeriya reshen jihar Bauchi yace yana raba wa kowane reshen banki naira miliyan N30m na sabbin takardun kuɗi a kowace rana domin su isa wurin al'umma cikin sauki.

Jami'in CBN, Mista Abdulkadir Jibrin, shi ne ya bayyana haka yayin da yake yawon sa ido a bankunan kasuwanci da ganin yadda abubuwa ke tafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel