CBN Na Raba Wa Bankuna Miliyan N30m Na Sabbin Naira a Kowace Rana

CBN Na Raba Wa Bankuna Miliyan N30m Na Sabbin Naira a Kowace Rana

  • CBN reshen jihar Bauchi ya yi kira ga ɗaukacin al'umma su kai korafin kowane banki ne suka ga babu kuɗi a ATM
  • Jami'in babban bankin, Abdulkadir Jibrin, ya ce a kowace rana suna ba kowane reshen Banki N30m domin saukaka wa kwastomomi
  • Yace kowane mutum ɗaya yana da damar musanya N10,000 zuwa kasa amma idan ya wuce haka sai dai ya bude asusun banki

Bauchi - Babban Bankin Najeriya reshen jihar Bauchi yace yana raba wa kowane reshen banki naira miliyan N30m na sabbin takardun kuɗi a kowace rana domin saukaka wa kwastomomi.

Jaridar Punch ta rahoto cewa wani Jami'in CBN, Mista Abdulkadir Jibrin, shi ne ya bayyana haka yayin da yake yawon sa ido a bankunan kasuwanci na jihar Bauchi ranar Litinin.

Sabbin takardun kuɗi.
CBN Na Raba Wa Bankuna Miliyan N30m Na Sabbin Naira a Kowace Rana Hoto: CBN
Asali: UGC

Mista Jibrin ya je duba yadda bankunan suke sakin sabbin takardun naira ga mutane musamman kwastomominsu masu amfani da ATM.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: CBN Ta Fara Sabon Tsarin da Mutane Zasu Ji Dadi Wajen Samun Sabbin Kuɗi

Ya ce an bullo da shirin ne domin tabbatar da sabbin kuɗin sun wadata a bankuna da kuma saukaka wa al'umma su musanya tsaffin kuɗin dake hannun su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Dubu 10,000 kaɗai ko ƙasa da haka za'a musanya wa kowane mutum ɗaya kuma idan adadin kuɗinka sun zarce haka, ya kamata ka buɗe asusun Banki."
"A kowace rana dukkan rassan bankuna na karban miliyan N30m domin tabbatar da sun zuba tsabar sabbin kuɗin a na'urar ATM ɗaiɗaikun mutane su sa katunansu su cire kuɗi."

Bayan haka ya roki ɗaukacin al'umma da su yi amfani da karin wa'adin kwanaki 10 kafin 10 ga watan Fabrairu, 2023 wajen mayar da tsaffin kuɗinsu zuwa bankuna domin guje wa asara.

"Wata ƙofa ce ga mutanen da ba su kai kuɗinsu banki ba da waɗanda ke da dubu N10,000 ko kasa da haka. Kwamitinmu zai ci gaba da zuwa wurin mutanen ƙauyuka ya nemi tsaffin kuɗi kana ya musanya masu da sabbi."

Kara karanta wannan

Abun Farin Cikin da Ya Faru da Yan Najeriya Bayan CBN Ya Kara Wa'adin Musanya Sabbin Kuɗi

Jibrin ya kara da bayanin cewa suna zuwa duba ATM ne domin tabbatar da bankuna na zuba kuɗi don mutane su cire domin shi ne kaɗai zai ba mutane damar samun sabon kuɗi.

A cewarsa ma'aikatan CBN zasu bi suna duba adadin kuɗin da ake sanya wa a ATM sannan ya yi kira da al'umma da su kai korafin duk bankin da ya ƙi fitowa aiki ko ya daina sanya sabbin kuɗi.

CBN Ya Fara Sabon Shirin Rabawa Talakawa Sabbin Kuɗi a Arewacin Najeriya

A wani labarin kuma CBN Ya Fara Musanya Wa Mutane Sabon Kudi a Jihar Sakkwato dake arewa maso yamma

Babban bankin Najeriya (CBN) ya fara shirin musanya wa mutane kuɗi su ba da tsoho a basu sabbbin takardun Naira uku da aka sauya a jihar Sakkwato.

Asali: Legit.ng

Online view pixel