Zan Tarwatsa Wajen Nan: Matashi Ya Dau Zafi a Banki Kan Tsoffin Kudade, Bidiyon Ya Yadu

Zan Tarwatsa Wajen Nan: Matashi Ya Dau Zafi a Banki Kan Tsoffin Kudade, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani matashi dan Najeriya ya yi barazanar tarwatsa wani banki kan rashin samun damar shiga ciki don yin hada-hadar kudi
  • Mutumin ya fusata lokacin da aka rufe kofar bankin sannan mai tsaron bakin ya hana shi shiga ciki
  • Yan Najeriya a TikTok sun sha dariyan bidiyon yayin da ake kara samun karancin sabbin kudin a kasar

Wani bidiyo da ya yadu ya nuno wani fusataccen matashi wanda ya dauki zafi lokacin da aka hana shi shiga wani banki.

Ya so ya shiga cikin bankin ne domin yin hada-hadar kudi amma sai ya zamana akwai cunkoson mutane a bankin.

Matashi da kudi
Zan Tarwatsa Wajen Nan: Matashi Ya Dau Zafi a Banki Kan Tsoffin Kudade, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@abeltech and Bloomberg/Getty Images.
Asali: UGC

Sai dai kuma, wani mai gadin banki ya tsare bakin kofar sannan ya hana shi shiga ciki. A nan ne mutumin ya kwance.

Ya fara ne da ihu sannan kuma ya yi barazanar tayar da zaune tsaye. Ya ce kada mai gadin da ya rufe kofar ya bari ya tarwatsa wajen.

Kara karanta wannan

Saura ranar aiki 1 kacal, CBN Tace Ta Fitar Da Sabbin Kudi N120m Jihar Katsina

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai gadin ya yi watsi da barazanar da yake yi sannan ya rufe masa kofa saboda bacin rai. Ba a tabbatar da abun da ya so yi ba, amma dai yan Najeriya da dama na ta fuskantar kalubale wajen saka tsoffin kudadensu a banki.

Bidiyon ya baiwa yan Najeriya da dama a TikTok dariya. Mutane da dama sun garzaya sashin sharhi don yin martani a bidiyon da @abeltech ya wallafa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Girl ta ce:

"Fuskar yarinyar nan. Ka san cewa zai yi wari ba kadan ba."

@ScárLétt ta yi martani:

"Ina nan ina jiran TikTok ya mayar da wannan ya zama sabon sauti."

@Moment ya ce:

"Idan wa'adin kudin nan ya kare a hannun mutumin nan toh akwai matsala."

@Abixzy ya ce:

Kara karanta wannan

Matashi Ya Nemo Tsohon Da Ke Ba Shi Alawa Shekaru 20 Da Suka Wuce, Ya Masa Gagarumin Kyauta

"Wanda ke da kudi shine yake fadan samun sabbin kudi. Ni da na san naira 70 ne kawai da ni.

Kasuwar bayan fage: Ana siyar da sabbin kudi don samun riba

A wani labarin, wasu masu tallar sabbin kudin sun mamaye tashar motar Dadi da ke karamar hukumar Sabon Garin Zaria, jihar Kaduna inda suke cinikinsu ba ji ba gani don samun tarin riba mai yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel