Muna Fama da Yunwa Kafin CBN Ya Kawo Dauki, Inji Mazauna Kauye Game da Batun Musayar Kudi

Muna Fama da Yunwa Kafin CBN Ya Kawo Dauki, Inji Mazauna Kauye Game da Batun Musayar Kudi

  • Mazauna kauye sun bayyana jin dadinsu ga yadda CBN ya kirkiro musu hanyar musayar kudi a yankunansu
  • Babban bankin Najeriya ya nada wakilai da za su zagaya lungu da sako don tabbatar da an rabu da tsoffin kudi
  • 'Yan Najeriya sun shiga damuwa a tun farko lokacin da wa'adin daina amfani da tsoffin kudi ya karato

Arewacin Najeriya - Wasu mazauna karkara sun shaida cewa, a baya suna cikin mayuwacin hali kafin babban bankin Najeriya (CBN) ya kawo musu dauki.

Idan baku manta ba, CBN da sauran bankunan kasuwanci sun tura wakilansu zuwa kauyuka domin musayar tsoffin kudade da sabbi ba tare da cajin ko Kobo ba.

A wata tattaunawa da jaridar Daily Trust, wasu amzauna sun bayyana mawuyacin halin da ya suka shiga kafin fara shirin musayar kudin.

Kara karanta wannan

Bayan Kara Wa'adi, CBN Ya Sake Fitar da Sanarwa Mai Muhimmanci Ga Yan Najeriya

Yadda 'yan kauye suka ji dadin kirkirar shirin musayar kudi
Muna Fama da Yunwa Kafin CBN Ya Kawo Dauki, Inji Mazauna Kauye Game da Batun Musayar Kudi | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Rayuwa ta yi kunci, CBN ya kawo dauki

Malam Muhammadu Bodinga na karamar hukumar Bodinga a jihar Sokoto ya bayyana cewa, rayuwa ta yi musu kunci sai kwatsam CBN ta kawo musu dauki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

“’Yan kasuwanmu sun daina karbar tsoffin kudade, wasu kam ma sun rufe shagunansu.
“Siyan abin da za a ci ma ya zama damuwa. Muna rayuwa cikin yunwa. Mun godewa CBN saboda baki da ya saka. Hakan ya taimaka mana.”

Mun gode bisa amsa kokenmu, basarake ga CBN

Hakimin Wamakko, Alhaji Aliyu Baraden Wamakko ya yabawa CBN bisa duba koken talakawa a irin wannan yanayi na bukatar taimako.

Ya shaidawa Daily Trust cewa:

“Sa bakin nan ya zo a kan lokacin da ya dace. Ya zo a lokacin da mutane ke tsananin bukatar taimako.”

A karamar hukumar Yabo ta jihar, sai da jami’an tsaro suka shiga tsakani wajen tabbatar da shirin musayar kudin tsakanin wakilan CBN da masu bukatar sabbin kudi.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'Sight and Sounds' Ta Shirya Taro Kan Manufofin Asiwaju Bola Tinubu

Hakazalika, wakilan na CBN sun shiga garuruwa a kananan hukumomin Shagari, Kware, Gwadabawa da Tambuwal na jihar ta Sokoto.

Majalisa ta yi fatali da batun kara wa'adi

A bangare guda, majalisar wakilai ta Najeriya ta bayyana bacin rai game da karin da CBN ya yi na daina amfani da tsoffin kudi.

Babban bankin ya bayyana kara wa'adin amfani da tsoffin kudi zuwa 10 ga watan Fabrarun 2023.

Ya zuwa yanzu dai majalisar na kan ra'ayin dole ta tattauna da gwamnan CBN don jin halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel