Kamen Murja Kunya: Za a Fara Yi Mata Gwajin Kwakwalwa Kafin Cigaba da Bincike

Kamen Murja Kunya: Za a Fara Yi Mata Gwajin Kwakwalwa Kafin Cigaba da Bincike

  • Hukumar 'yan sandan birnin Kano ta umarci yi wa Murja Ibrahim Kunya gwajin kwakwalwa kafin a cigaba da bincikarta
  • Kamar yadda aka gano, an kama budurwar 'yar TikTok din a ranar Lahadi bayan korafin da majalisar malamai ta Kano ta kai wa 'yan sanda
  • Bayan kama ta a otal inda ta ke kokarin shirya gagarumin bidirin ranar zagayowar haihuwarta, Murja tace ta tuba ta daina zagin jama'a

Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano tayi umarnin fara yi wa Murja Ibrahim Kunya, fitacciyar 'yar TikTok da suka kama a jihar, gwajin kwakwalwa da farko don gane ko hankalinta daya.

Murja TikTok
Kamen Murja Kunya: Za a Fara Yi Mata Gwajin Kwakwalwa Kafin Cigaba da Bincike. Hoto daga @realmurjaibrahim
Asali: Instagram

Mamman Dauda, kwashinan 'yan sandan jihar ne ya bada wannan umarnin kamar yadda SP Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya bayyana a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Kanawa Sun Yi Bore, Rikici Ya Barke a Jihar Kano Bayan Ziyarar Buhari

Kiyawa ya sanar da cewa, sai har an gudanar da gwajin kwakwalwar kan matashiyar mai shekaru 24 kafin 'yan sandan su cigaba da bincike.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ranar Lahadi ne dai runduna 'yan sandan jihar Kano suka yi ram da Murja Ibrahim Kunya bayan sun samu korafi kan yadda ta ke zage-zage tare da bata tarbiya a dandalin sada zumunta na TikTok.

An yi caraf da Murja a fitaccen otal na Tahir Guest Palace da ke birnin yayin da ta ke shirin gagarumin shagalin bakin ranar zagayowar haihuwarta.

An tattaro yadda majalisar malamai ta jihar Kano ta kai karar Murja wurin 'yan sandan kan bidiyoyinta da ta ke saki a dandalin TikTok din yadda suka sabawa addunin Islama.

Murja daga baya ta fito tayi alkawarin cewa ta tuba kuma ta daina zage-zage kamar yadda aka bukata.

Kara karanta wannan

Har Yanzu Buhari Bai Yi Magana Kan Kisan Fulani Da Bam Ba, Allah Wadai Wallahi: Miyetti Allah

Wannan kamen da 'yan sanda suka yi ya raba jama'a gida biyu inda wasu ke hankoron a sako ta yayin da wasu ke cewa ya zama tilas a ladatar da ita.

Sanannen abu ne yadda fitacciyar budurwar ke zage-zage da cin mutuncin duk wanda ya shiga harkarta a dandalin.

Ta kan hada da hoton mutum ba tare da tsoro ko shayi ba tayi bidiyo tare da kama sun ta dinga dura ashar da zagi masu cike da batsa.

Wannan lamarin ba malamai kadai ba, yana ci wa jama'a tuwo a kwarya don ganin yadda ya kasance barazana ga tarbiyyar yara masu tasowa nan gaba.

Daga ganinta na san na samu mata, Bakar Fata da Yayi wuff da baturiya

A wani labari na daban, wani matashi 'dan kasar Uganda ya sanar da yadda ya hadu da baturiyar da ya aura.

Ya sanar da cewa sun haduwa wurin bikin abokinsa inda yaje daukar hoto kuma yana ganinta ya san ya samu abokiyar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel