Daga Ganin Jar Fatar Nan Nasan Matata ce: Bakar Fata Ya Bada Labarin Haduwarsa da Matarsa Baturiya

Daga Ganin Jar Fatar Nan Nasan Matata ce: Bakar Fata Ya Bada Labarin Haduwarsa da Matarsa Baturiya

  • Zuciyar wani mutum daga Uganda ta darsu da son wata kyakkyawar mata 'yar Mzungu da ya hadu da ita a bikin gabatarwan auren wata abokiyarsa
  • James Mafabi, wanda ya halarci taron a matsayin mai daukar hoto ya ce ya ji a jikinsa Gemma Bevington matarsa ce
  • Mafabi, wanda abokansa ke kiransa da Jam jim ya ce, ya shigar da bukatar aurensa ga Gemma a rana ta hudu da suka hadu, inda ta amince

Ba kasafai mutane suke tambayar "Zaki amince ki aure ni?" bayan sanin juna na 'yan kwanaki ba.

Zasu so sanin juna sosai, abun da suke so, abun da ke burgesu, halayyarsu da danginsu da sauran abubuwa kafin su fara tunanin aure.

Baturiya da miji
Daga Ganin Jar Fatar Nan Nasan Matata ce: Bakar Fata Ya Bada Labarin Haduwarsa da Matarsa Baturiya. Hoto daga Monitor
Asali: UGC

Wannan lamarin ya sha bamban ga wasu ma'aurata da ke jin dadin rayuwar aurensu, inda basu dauki lokaci mai tsawo ba kafin su yi aure.

Kara karanta wannan

Borno: ISWAP Sun Yi Rabon Tsofaffin Kudi ga Fasinjojin Motocin Haya Kyauta, Sun ce SU je Bankuna Su Canza su

Masoyan biyu sun hadu ne a bikin gabatarwan auren abokinsu a Namakwekwe na Mbale da ke gabacin Uganda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wani aboki na ya bukaci in zo Uganda don halartar bikinsa."

- Gemma wacce ta ziyarci Afirka a karo na farko ta bayyana hakan, kamar yadda Monitor ta ruwaito.

Mafabi ya halarci taron gabatarwan a matsayin mai daukar hoto ba tare da sannin zai hadu da abokiyar rayuwarsa ba.

Duka biyun sun ce suna addu'ar samun masoya ba tare da sanin ranar ce zasu hadu da abokan rayuwarsu ba.

"Ina tuna lokacin da na shiga daki cike da mata suna gyara gashinsu. Nan take, idanuwa na suka hango ta. A zuciyata wani abu ya fada min, 'wannan matata ce'.
"Har cikin raina, na ji a jiki na ita ce za ta zama matata wata rana. A koda yaushe ina rokon Ubangiji da ya bani mata farar fata, tabbas Ubangiji ya amsa addu;ata."

Kara karanta wannan

Bidiyo: 'Dan Najeriya Ya Bayyana Wurin Biki da Akwatin Shakare da Sabbin Takardun Naira, Yana ta watsa Bandira

- A cewar Mafabi.

Yayin kwashe mahimman lokuta tare, daga nan ne suka 'dan zanta yayin da ake cigaba da shagalin, a nan ne Mafabi ya ba Gemma lambarsa.

"Bayan haduwa da ita a wurin, mun kai yamma muna tare. Haka za mu tuka kanmu zuwa Kamfala washe gari kafin ta koma (Babban birnin Amurka) a rana ta hudu, na bata mamaki da shigar da bukatar aure inda ta amince."

- Ya tuna.

Watanni uku bayan nan, suka fara shirye-shiryen biki wanda ya gabata a ranar 16 ga watan Disamba, 2022.

'Dan Najeriya ya je wurin Biki da akwatin kudim ya dinga watsa sabbin Naira

A wani labari na daban, wani 'dan Najeriya ya halarci wata liyafar aure da akwatin sabbin kudin Najeriya.

Daga isarsa ya garzaya gaban ango da amarya inda ya dinga wurga musu bandiran kudaden matsayin liki

Asali: Legit.ng

Online view pixel