‘Yan Fashi Sun Bindige Mai Sana’ar POS a Wajen Neman Sababbin Takardun Kudi

‘Yan Fashi Sun Bindige Mai Sana’ar POS a Wajen Neman Sababbin Takardun Kudi

  • Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun auka shagon wani mai sana’ar POS, sun harbe shi da bindiga
  • ‘Yan fashi da makamin sun sulale da makudan kudi daga shagon, sannan sun harbe wasu mutanen
  • Kwamishinan ‘yan sanda ya ziyarci wurin kafin Gwamna Bala Mohammed da kan shi ya je jaje a garin

Bauchi - Wani mummunan labari da muka samu shi ne na harbe wani Bawan Allah da ya ke yin sana’ar POS a karamar hukumar Zaki a jihar Bauchi.

A ranar Litinin ake zargin wasu ‘yan fanshi sun aukawa wannan ‘dan kasuwa mai sana’ar POS, suka bindige shi da rana, Vanguard ta kawo rahoton.

‘Yan fashin sun yi sanadiyyar yin wannan aika-aika ne saboda su na neman sababbin takardun kudi da babban bankin Najeriya na CBN ya buga.

Kara karanta wannan

Kamfe Ya Tsaya Babu Shiri Bayan An Kora ‘Yar Takarar M/Gwamna da Ta je Yakin zabe

Baya ga harbin 'dan kasuwar, jaridar ta ce ‘yan fashi da makamain ba su tsaya nan ba, sun harbe wasu mutane wadanda suka zo neman kudi a shagon.

Kwamishinan 'yan sanda ya yi magana

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Aminu Alhassan ya tabbatar da aukuwar lamarin a fadar Galadiman Katagum, Usman Mahmood Abdullahi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin farin cikin shi ne Aminu Alhassan ya shaida cewa ba a rasa rayuka ba. A gidan rediyon Najeriya, an ji Kwamishinan ya yi alkawarin yin bincike.

Gwamna
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed Hoto: radionigerianortheast.gov.ng
Asali: UGC
“Wadanda abin ya shafa sun je neman sababbin kudi ne sai ‘yan bindigan suka auka masu, suka buda masu wuta domin tsora mutane.
Da yardar Ubangiji, za mu cigaba da yin bakin kokarinmu wajen cafke wadanda suka yi wannan danyen aiki wanda yanzu sun tsere.”

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga Sun Shiga Gida, Sun yi Nasarar Awon Gaba da Hakimi a Arewacin Najeriya

- CP Aminu Alhassan

Jajen Bala Mohammed

Tribune ta ce Mai girma Gwmanan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ziyarci fadar Katagum domin yi masu jajen wannan lamari da ya auku a cikin kasarsu.

Gwamna Bala Mohammed ya yi kira ga Kwamishinan ‘yan sanda da aka kara adadin jami’an tsaro da ke yankin Zaki domin hana faruwar irin haka nan gaba.

Ana zargin ‘yan fashin sun yi nasarar dauke N7m daga shagon ‘dan kasuwar da ke tashar mota.

Abdullahi Mustapha wani mai sana'ar POS a garin Zariya a jihar Kaduna ya shaidawa Legit.ng Hausa ana fuskantar barazana saboda tsarin da aka kawo.

'Dan kasuwan ya ce mana samun kudi yana wahala a dalilin canza kudi da takaita yawon kudi, yake cewa hakan ya jawo kasuwancinsu ya tsaya cak yanzu.

Sharrin Boko Haram

An ji labari Muhammadu Buhari ya ce akwai badakala a cikin lamarin ‘Yan kungiyar ta’addan Boko Haram da suka addabi Najeriya a 'yan shekarun bayan nan.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari, Sun Harbawa Mutane Bama-Baman Roka a Jihar Zamfara

Shugaba Muhammadu Buhari yake cewa ya na zargin akwai wata kungiya daga kasashen waje da ke sha’awar ruguza kasar nan mai goyon bayan aikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng