Saura Kwana 120 Ya Bar Mulki, Buhari Ya Yi Fallasa a Kan ‘Yan Ta’addan Boko Haram
- Muhammadu Buhari ya tunawa jama’a halin da aka damka masa mulkin Najeriya a Mayun 2015
- Shugaban kasar ya ce kananan hukumomi 4 ne kurum ba su hannun Boko Haram da ya shiga ofis
- A jawabin da ya yi a Kano, Buhari ya ce duk da karancin kudi, ya gina abubuwan more rayuwa
Kano - Shugaba Muhammadu Buhari ya fito ya bayyana cewa yana zargin akwai hannun kungiyoyin ketare a kan harkar ta'addancin Boko Haram.
Vanguard ta rahoto Mai girma shugaban kasar yana zargin kungiyoyin kasashen waje da ke da nufin karya kasar nan da laifin assasa Boko Haram.
Muhammadu Buhari ya yi wannan bayani ne a wajen wata liyafar da gwamnatin jihar Kano ta shirya masa a ranar Litinin, 30 ga watan Junairu 2023.
A farkon makon nan Shugaban kasar ya ziyarci garin Kano domin bude wasu ayyuka da gwamnatin tarayya da kuma Dr. Abdullahi Umar Ganduje suka yi.
Boko Haram a 2015
A jawabin da ya gabatar wajen cin abincin, Mai girma Buhari ya tunawa Kanawa irin halin da ya tsinci Najeriya a lokacin da ya hau mulki a Mayun 2015.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jaridar ta ce shugaban Najeriyan mai ragowar kwanaki 121 ya ce kafin ya karbi mulki, gwamnati ba ta da iko da mafi yawan garuruwan jihar Borno.
“A lokacin da muka hau mulki a 2015, Boko Haram su na da iko da kananan hukumomi 13 daga cikin 27, hudu ne kurum ke hannun Gwamnati.
Baya ga haka kuma, rabin kananan hukumomin jihar Yobe su na karkashin 'Yan Boko Haram.
A yau da taimakon Gwamna mai kwazo da kishi na jihar Borno, an karbe duka kananan hukumomin.
Su wanene Boko Haram? Akwai badakala a cikin lamarin. Ina zargin akwai wata kungiyar kasar waje da ke sha’awar ruguza Najeriya ne.
Idan ba haka ba, ta ina Boko (ilmin zamani) zai zama haramun?
Sahara Reporters ta ce Buhari ya yi bayanin yadda gwamnatinsa tayi kokari wajen samar da abubuwan more rayuwa a kasar nan, duk da karancin kudi.
A karshen jawabinsa, shugaban kasar ya godewa ‘Yan Najeriya da suka mara masa baya ya yi mulki.
Buhari a Kano
An samu labari cewa Shugaban kasar Najeriya bai karaya a kan rade-radin barazanar tsaro a Kano ba bayan abin da ya faru da shi a jiharsa ta Katsina.
Jama’a na ta tofa albarkacin bakinsu game da wannan ziyara ta Muhammadu Buhari zuwa Garin Kano wanda da farko mutane sun yi tunanin za a fasa.
Asali: Legit.ng