Ku Ba Ni Dama Na Gyara Najeriya Ta Dawo Sabuwa, Obi Ga Magoya Bayansa a Borno

Ku Ba Ni Dama Na Gyara Najeriya Ta Dawo Sabuwa, Obi Ga Magoya Bayansa a Borno

  • Yan makonni kafin zabe, Peter Obi ya roki masu zabe da su ba shi damar kawo chanjin da ake bukata a Najeriya
  • Obi ya ce dukkanin yan Najeriya za su sha romon dadi idan har ya zama magajin Buhari a zaben watan gobe
  • Dan takarar na LP ya ba al'ummar arewa tabbacin kawar da talauci daga yankin ta hanyar basu ilimi da inganta noma

Borno - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi, ya bukaci mutanen jihar Borno da su ba shi dama ya farfado da Najeriya inda mutane za su samu damammaki daidai da kowa.

Da yake magana a wajen gangamin kamfen dinsa a ranar Asabar, 28 ga watan Janairu a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, Obi ya bayyana cewa sauran jam'iyyu sun gaza.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Kai Ziyarar Bazata Kudancin Borno, Ya Kafa Tarihi

Ya ce lallai ya kamata yan Najeriya su ba jam'iyyar LP dama don samar da chanjin da ake bukata, Arise News ta rahoto.

Peter Obi
Ku Ba Ni Dama Na Gyara Najeriya Ta Dawo Sabuwa, Obi Ga Magoya Bayansa a Borno Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna so ku rike mu don samun Najeriya sabuwa. Tsawon lokaci mutane na ta lalata makomar yan Najeriya kuma ba zai yiwu mu ci gaba a haka ba.
"Za mu kare sannan mu farfado da Najeriya zuwa yadda ya kamata ta kasance."

Zan bunkasa noma da ilimantar da yan arewa don fitar da su daga kangin talauci, Obi

Obi wanda ya koka kan kalubalen rashin tsaro a Borno da sauran yankunan Najeriya, ya ce gwamnatinsa za ta farfado da muradin mutane da kuma tabbatar da ganin cewa yan Najeriya basu tsaya a sansanin yan gudun hijira ba.

Ya ce Borno tana da yalwar filayen noma da albarkatu wanda idan aka yi amfani da su yadda ya dace za su samar da biliyoyin naira duk shekara.

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Yi Magana Kan Zaben 2023, Ya Aika Sako Mai Muhimmanci Ga Kiristoci A Najeriya

Ya kara da cewar:

"Gwamnatina ta yi wa arewa babban tanadi, musamman a bangaren noma da ilimi da zai taimaka wajen fitar da su daga talauci."

A nashi bangaren, dan takarar mataimakin shugaban kasa na LP, Datti Baba-Ahmed, ya magantu a kan tarihin da Obi ya kafa a matsayin gwamna, yana mai cewa bai ranci kudi don yi wa jihar aiki ba.

Ya ce manyan jam'iyyun kasar biyu sun gazawa yan Najeriya don haka LP ce mafita don ceto kasar.

APC ce za ta lashe zabe mai zuwa, Tinubu

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce zai lallasa sauran abokan hamayyarsa a zabe mai zuwa duk da makarkashiyar da ake masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel