Tinubu Ya Bayyana Irin Taimakon da Ya Kaiwa Atiku Yayin da Obasanjo Yaso Ganin Bayansa

Tinubu Ya Bayyana Irin Taimakon da Ya Kaiwa Atiku Yayin da Obasanjo Yaso Ganin Bayansa

  • Bola Tinubu ya sanar da cewa, cetonsa da yayi wa Atiku ne ya kubutar da shi yayin da Obasanjo ya tasarwa ganin bayansa a rikicin da suka yi
  • Ya sanar da cewa, a kowanne lokaci faduwa ya ke, Buhari, Jonathan, Obasanjo duk sun mutsuka Atiku kuma sun ci riba tare da zama lafiya
  • Ya shawarci mazauna Akwa Ibom da su guji zaben Atiku saboda hatta bishiyoyin kwakwa da suke tunkaho dasu sai ya siyar

Uyo, Akwa Ibom - Bola Tinubu, 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, yace da kanshi ya ceci Atiku Abubakar yayin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya tasarwa ganin bayansa.

Tinubu da Atiku
Tinubu Ya Bayyana Irin Taimakon da Ya Kaiwa Atiku Yayin da Obasanjo Yaso Ganin Bayansa. Hoto daga Thecable.ng
Asali: UGC

Abubakar, tsohon shugaban kasa kuma yanzu 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya dinga samun matsaloli da ubangidansa na tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu, Obi: An Shiga Fargaba Yayin da Malamin Addini Ya Aika Gagarumin Gargadi Ga Manyan Yan Takarar Shugaban Kasa

Dukkansu sun samu sasanci a yayin da ake shirin fara zaben 2019, jaridar TheCable ta rahoto.

Obasanjo ya bayyana goyon bayansa ga Abubakar don takarar shugabancin kasa a zaben 2019 inda yace ya fi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke mulki a lokacin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, a yayin da ake gangamin zaben shugaban kasa na 2023, tsohon shugaban kasan tuni ya bayyana goyon baynsa ga Peter Obi, 'dan takarar Labour Party.

A yayin jawabi a kamfen dinsa a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, tsohon gwamnan jihar Legas din yace Abubakar da jam'iyyarsa duk neman na cika kundunsu suke.

"Ya tsere zuwa Dubai kuma yayin da zabe ya zo, ya sake dawowa saboda samun na cika ciki. Ya zo Legas, mun gyara shi tare da bashi tikiti amma bai yi amfani da shi yanda ya dace ba sai ya karba kudi.

Kara karanta wannan

'Barin Zance: Gwamnonin APC 3 Sun Jagoranci Tinubu Domin Kai Wa Buhari Ziyarar Dannar Ƙirji

"Ya fuskanci Obansajo, ya fuskanci Buhari kuma duk babu nasara. Ya kasa yi da Jonathan. A dukkan lamurransa faduwa yake yi.
"Gara ku kula da shi kafin ya fara siyar da bishiyoyin kwakwa da suka rage. Abinda mu ke bukata shi ne habaka kasar nan. Muna da isassan iskar gas.
“Akwai Ibom, ba za ku wahala ba. yaro Emmanuel Udom da ya kawo Atiku nan, da ya ke kiran kansa Gwamna, ku fada masa ya isa haka. A bayan gidana ya ke zama a Legas. Ba don mun zama daya ba, da na kora shi gida."

- Yace.

Buhari ya nada Dogara matsayin sabon DG na NYSC

A wani labari na daban, Shugaba Buhari ya amince da nadin Birgediya Janar Ahmed Dogara matsayin sabon darakta janar na NYSC.

Wannan na zuwa ne bayan da ya fatataki Fadah daga shugabancin hukumar a watanni uku da suka gabata saboda rashin kwazo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel