Sabbin Naira: Rikici ya kunno kai tsakanin Buhari da majalisa kan kara wa'adin daina amfani da tsoffin kudi

Sabbin Naira: Rikici ya kunno kai tsakanin Buhari da majalisa kan kara wa'adin daina amfani da tsoffin kudi

  • An samu rabuwar kai tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da majalisar wakilai kan wa'adin daina karbar tsoffin kudi
  • Buhari ya amince da bukatar gwamnan babban bankin kasa na kara wa'adin kwanaki 10 na daina amfani da tsoffin kudi
  • Majalisar wakilai ta yi watsi da lamarin, ta ce lallai sai dai a kara wa'adin watanni shida nan gaba

Abuja - Takaddama na shirin shiga tsakanin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da majalisar wakilai kan wa'adin daina amfani da tsoffin kudi, rahoton Vanguard.

Da farko dai babban bankin Najeriya, CBN ya bayar da wa'adin 31 ga watan Janairu don daina amfani da tsoffin takardun kudi na N200, N500 da N1000 tare da maye gurbinsu da sabbi.

Sai dai kuma, a jiya Lahadi, 29 ga watan Janairu ne shugaban kasar ya bukaci CBN da ya amince da karin wa'adin kwanaki 10 a kan wanda ya bayar wato ranar 10 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Majalisa ta yi martani mai zafi bayan kara wa'adin kashe tsoffin kudi a Najeriya

Batun sabbin kudi ya gwara kan Buhari da 'yan majalisa
Sabbin Naira: Rikici ya kunno kai tsakanin Buhari da majalisa kan kara wa'adin daina amfani da tsoffin kudi | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

An kuma kara wasu kwanaki bakwai, 10 ga watan Fabrairu zuwa 17 ga watan Fabrairu don ba yan Najeriya damar shigar da tsoffin kudadensu a CBN bayan wa'adin Fabrairu lokacin da za a daina amfani da tsoffin kudaden a matsayin halastacce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, majalisar wakilai ta yi watsi da karin wa'adin tana mai cewa dole CBN ya bi shawararta na kara wa'adin watanni shida.

Buhari ya amince da wa'adin - Emefiele

Shugaban kasar ne ya amince da karin wa'adin kwanaki 10 bayan ganawarsa da gwamnan babban bankin kasar, Mista Godwin Emefiele, mahaifar Buhari a Daura, jihar Katsina a ranar Lahadi.

Shugaban kasar ya amince da bukatar Emefiele a lokuta barkatai domin ba yan Najeriya damar sauya kudadensu zuwa sabon da aka sauya, da kuma rage yuwuwar samun asara a tsakanin mazauna yankunan karkara.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ganduje ya Bayyanawa Buhari Matsayar Kanawa Kan Ziyarar da Zai Kai Jihar

Emefiele ya yi jawabi ga manema bayan taron, yana mai bayyana cewa an dawo da kas0 75 cikin dari na naira tiriliyan 2.7 da aka rika a wajen tsarin bankuna, inda aka samu ragowa a hauhawan farashin kayayyaki da karin daidaito a farashin canjin kudaden waje.

Haka kuma ya ce lamarin ya yi tasiri sosai a bangaren tsaro, musamman a bangaren fashi da makami da garkuwa da mutane.

Majalisar wakilai ta dauki dumi, ta ce dole a bi doka yadda ya kamata

Ku tuna cewa a makon jiya majalisa ta bukaci a kara wa'adin daina karbar kudin da watanni shida.

Majalisar ta kuma kafa kwamitin wucin gadi karkashin jagorancin Ado Doguwa domin duba batun rashin wadatar kudin tare da gwamnan CBN da shugabannin bankuna.

A cikin sanarwar da ke watsi da batun karin wa'adin kwanaki 10 da Buhari ya amince da shi a jiya Lahadi, Doguwa ya ce sam hakan ba shine mafita ba, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Saura ranar aiki 1 kacal, CBN Tace Ta Fitar Da Sabbin Kudi N120m Jihar Katsina

Doguwa ya ce kwamitinsa zai ci gaba da aiki har sai ya cika muradan yan Najeriya daidai da dokar kasar.

Da yake bayyana karin wa'adin a matsayin siyasa don ci gaba da yaudarar yan Najeriya da lalata tattalin arziki da hanyar samun abincinsu, Doguwa ya ce manufar na iya kawo tangarda ga zabe mai zuwa.

Ya kara da cewa, majalisa za ta ba da izinin kama gwamnan na CBN idan ya ki bayyana a gaban kwamitin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel