Zuciyoyi Sun Karaya Yayin da Gwamna Sule ke Kwararawa Gawar 'Dansa Addu'a, Hoto ya Bayyana

Zuciyoyi Sun Karaya Yayin da Gwamna Sule ke Kwararawa Gawar 'Dansa Addu'a, Hoto ya Bayyana

  • An matukar tausayawa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa bayan hoton lokacin da ya ke kwararawa gawar 'dansa da ya rasu addu'a
  • An rahoto cewa, Gwamnan ya rasa babban 'dansa a sa'o'in farko na ranar Juma'a da ta gabata, bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita
  • Ayoola, wani 'dan Najeriya ne ya wallafa hoton yayin da gwamnan ke addu'a kan gawar 'dansa inda yace jarabawa ce daga Allah wacce ta wuce kudinsa da matsayinsa

Lafia, Nasarawa - An ga yadda gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya ke makoki a wani hoto inda ya ke gaban gawar babban 'dansa, Hassan Sule, yana kwarara masa addu'a.

Hassan Sule ya kwanta dama a safiyar Juma'a, 27 ga watan Janairun 2023 bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita a Lafia, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Hoto: Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Gwamnan Nasarawa Ke Yi Wa Gawar Dansa Addu’a

Gwamna Sule gaban gawar 'dansa
Zuciyoyi Sun Karaya Yayin da Gwamna Sule ke Kwararawa Gawar 'Dansa Addu'a, Hoto ya Bayyana. Hoto daga @AYOOLA007
Asali: Twitter

Gwamna Sule yana kwararawa gawar Hassan addu'a

Wani wanda ke taya shi makoki mai amfani da @ayoola007 ya je shafinsa na Twitter inda ya wallafa hoton lokacin da ya ke addu'ar tare da fatan Allah ya bai wa iyalan hakurin rashin da suka yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Wannan gwamna ne da ke kan mulki ya ke addu'a a kan gawar babban 'dansa. Jarabawar Allah ta fi karfin dukiya da matsayi. Alhha kasa kada jarabawarmu ta fi karfinmu."

Ga wallafar:

Hassan ya rasu yana shekarun samartakarsa ta 36 a duniya. Wasu 'yan Najeriya sun gangara sashin sharhi inda suka dinga jajantawa gwamnan da iyalansa.

Ga wasu daga cikin martanin

"Allah ya kara masa karfin guiwa kuma ya ba iyalan hakuri. Babu uban da ya cancanta ya birne 'dansa. Kamata yayi shi ya birne shi," @naijateddy tace.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule: Jajiberin 'Dana Zai Rasu, Na Dinga Rarrashin Mahaifin da ya Rasa Yara 9 da Shanu 70 a Tashin Bam din Nasarawa

"Allah ya yafe masa kuma yayi masa rahama. Allah ya bai wa masoyansa hakuri tare da basu hakurin jure wannan rashin. Ameen," @hafidaibrah yace.

Paul Ikenna Esq. ya kwatanta hoton da:

"Hoto mafi taba zuciya da na taba gani kenan."

Toyin. SM. Adeyemi tayi addu'a ga iyalan da gwamnan da su kasance masu kwarin guiwa. Tace:

"Ubangiji ka kawo rahama, ka saukakawa wannan mahaifin da dukkan iyalsan. Babu iyayen da suka cancanci wannan makokin. Ina muku ta'aziyya, ka yi hakuri ran ka shi dade."

Na gama rarrashin wanda ya rasa yara 9 da shanu 70 kenan Hassan ya rasu, Gwamna Sule

A wani labari na daban, Gwamna Sule na jihar Nasarawa ya sanar da yadda ya dinga rarrashin wani mahaifi da ya rasa yaransa 9 da shanu 70 a bam din da soji suka saki a jihar ana gobe Hassan zai rasu.

Ya sanar da cewa jarabawa ce Allah ya kawo masa kuma gwajin imaninsa ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel