Bidiyo: Matar Aure Tayi Kicibus da Mijinta da Budurwarsa Sun Shakatawa Wurin Cin Abinci

Bidiyo: Matar Aure Tayi Kicibus da Mijinta da Budurwarsa Sun Shakatawa Wurin Cin Abinci

  • Wata mata 'yar Najeriya a cikin kwanakin nan ta kama mijinta dumu-dumu yana sharholiya da budurwarsa a wani gidan abinci a Port Harcourt
  • A wani bidiyo da ya yi tashe, matar wacce ke sanye da wata hadaddiyar rigar da ke bayyana surar jikinta ta ritsa mijinta a wurin cin abinci
  • Mijin na ta, tare da taimakon wani jami'in tsaro da ke wurin ya yi kokarin natsar da ita amma hakan bata yuwu ba saboda ta fusata

Wata mata 'yar Najeriya jikinta ya mutu murus bayan ritsa mijinta dumu-dumu da budurwarsa su na sharholiya a wani gidan abinci.

Matar Aure
Bidiyo: Matar Aure Tayi Kicibus da Mijinta da Budurwarsa Sun Shakatawa Wurin Cin Abinci. Hoto daga @torifor9jatown
Asali: Instagram

An tattaro yadda matar auren ta gaggauta tara jama'a yayin da ta yi ido biyu da mijinta da wata mata a Kilimanjaro.

A bidiyon, matar wacce ta ke sanye da wata riga da ke bayyana kowanne lungu da sako na jikinta, ta yi hargowa da karfin muryarta yayin da ta jefi mijin nata da zafafan kalamai.

Kara karanta wannan

Bidiyon Dirarriyar Amarya Mai Shekaru 57 da ke Nuna Yarinta, Ta Saka Jar Riga ta Amaren Zamani

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin martani game da karajin da ta ke yi, ya yi kokarin natsar da ita gami da ce ma ta tazo su koma gida kada su raba hali, duk a bidiyon da @torifor9jatown suka wallafa a Instagram

Haka zalika, wani jami'in tsawo ya shiga maganar amma duk da haka ta yi kunnen uwar shegu da su, yayin da matar auren ta riga ta kai wuya.

Martanin 'yan soshiyal midiya

@leemt_detoro ta ce:

"Dubi mace iya mata, wai me maza suke so ne wai."

@surestdiva ta ce:

"Idan ni ce zan bukaci a kawo min duk wani abu da ke gidan abincin in sa ya biya. Ni ba wacce wani namiji zai sa wa damuwa bace."

@c.h.u.r.c.h.i.l ya yi martani:

"Ya kamata ku dinga girmama matanku."

@amaka_nne ta ce:

Kara karanta wannan

Bidiyo: Ana Tsaka da Shagalin Aure, Takardar da Wani ya Mikawa Amarya ta Tada Hankalin Ango

"Duk da ba a kaina abun ya faru ba, anma ba na tunanin zan ko bashi amsa a wurin. Kawai mu je gida ne, ni ba wacce zai kashe bace."

@joycelynoge ya yi martani:

"Wai me yasa ake ta dora laifi ga bangare daya ne?"

@chumsy296 ta yi martani:

"Wulakantattatun mutane, mtcheew."

@vivian.richgirl ta ce:

"Amma matar zazzafa ce, to wai me maza suke so ne?"

@eddidiong_richardz ya yi kari:

"Mazan auren Port Harcourt kenan."

@goodlover100 ta ce:

"masoyi yana ruwa cikin tabo."

Daga mikawa amarya takarda, hankalin ango ya tashi

A wani labari na daban, wani ya mikawa wata amarya takarda a wurin shagalin bikinsu inda hakan ya tada hankalin ango.

Amaryar ta bude inda ta gta fatan alheri ake musu kan aurensu sannan ta mikawa angon, hakan ya kwantar masa da hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel