Zai Janyewa Atiku: Sarakuna da Limaman Arewa Na Tattaunawa Da Kwankwaso

Zai Janyewa Atiku: Sarakuna da Limaman Arewa Na Tattaunawa Da Kwankwaso

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Atiku Abubakar na iya samun karin karfi a yan kwanaki masu zuwa
  • Rahotanni sun kawo cewa Sanata Rabiu Kwankwaso na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na iya hadewa da Atiku
  • Ana ganin wannan ci gaban na iya kawo cikas ga damar da Bola Ahmed Tinubu ke da shi a yankin arewa

Gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023, shugabannin arewa sun yi karin bayani game da yiwuwar Sanata Rabiu Kwankwaso na jam'iyyar Nigeria Peoples Party (NNPP) ya janyewa takwaransa na Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar.

A ranar Lahadi, 29 ga watan Janairu, dattawan arewa sun nuna yakinin cewa Sanata Kwankwaso zai rushe tsarinsa don goyon bayan takarar shugabancin Atiku, rahoton Independent.

Rabiu Kwankwaso da Atiku Abubakar
Zai Janyewa Atiku: Sarakuna da Limaman Arewa Na Tattaunawa Da Kwankwaso Hoto: Rabiu Kwankwaso da Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Koda dai Kwankwaso da NNPP sun sha nanata cewa basu da niyan janyewa kowani dan takara domin suna so su gwabza da takwarorinsu a babban zaben mai zuwa a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Sakataren NNPP Ya Fallasa Asirin Kwankwaso, Ya Faɗi Abubuwa Da Yawa

A yayin ziyarar da ya kai Lagas a 2021, an tambayi Kwankwaso ko yana da niyan janyewa wani sai ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"NNPP ta fito don lashe babban zaben 2023. Kada wani ya yi tunanin wani a cikinmu zai janye a wannan mataki da aka kai. Na shirya mahawara da dukkanin yan takara."

Yayin da yake jawabi a Chatham House a kwanan nan, tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce babu yadda za a yi ya janywa kowani dan takara. Ya ce shine ya fi cancanta da aikin.

Ana gab da cimma yarjejeniya tsakanin Kwankwaso da Atiku, Kungiyar dattawan arewa

Da yake magana game da yuwuwar Kwankwaso ya rushe tsarinsa ma Atiku, jigon kungiyar dattawan arewa ya fada ma jaridar Daily Independence cewa kwanan nan za a cimma wata yarjejeniya tsakanin jam'iyyun biyu.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu, Obi: An Shiga Fargaba Yayin da Malamin Addini Ya Aika Gagarumin Gargadi Ga Manyan Yan Takarar Shugaban Kasa

Ya bayyana cewa hadaka tsakanin bangarorin biyu ya zama dole kasancewar zai taimaka wajen kawo karshen tsanar da Atiku ke fuskanta daga tsagin Nyesom Wike wato gwamnonin G-5.

Jigon kungiyar dattawan na NEF wanda aka sakaya sunansa ya ce masu ruwa da tsaki a arewa sun rigada sun fara tattaunawa da Kwankwaso.

Ya bayyana cewa shugabannin addini, tsoffin Janarori, da sarakuna sun fara yunkurin lallashin Kwankwaso don ya janye.

Akwai aiki ja a gabanku, malamin addini ya gargadi manyan yan takarar shugaban kasa

A wani labarin, mun ji cewa shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Ayodele ya bayyana wasu kalubale da manyan yan takarar shugaban kasa za su fuskanta gabannin zabe mai zuwa.

Ya ce dole sai sun tashi tsaye tsayin daka don tunkarar abubuwan da ke fuskanto su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel