Kwantenar Kaya Ta Rikito Kan Motar Haya a Legas, Mutum 9 Sun Ce Ga Garinku

Kwantenar Kaya Ta Rikito Kan Motar Haya a Legas, Mutum 9 Sun Ce Ga Garinku

  • Kuma dai! Wani kwantena ya sake fadawa kan motar haya cikin garin Ojuelagba a Legas
  • Hukumar bada agaji na gaggawa ta LASEMA da jami'anta sun dira wajen domin ceto wadanda ya afka da su
  • Abin takaici mafi akasarin wadanda ke cikin motar basu da sauran kwana a gaba

Legas - Akalla fasinjojin motar Bas tara ne suka rasa rayukansu yau Lahadi karkashin gadar Ojuelegba dake jihar Legas inda kwantena ta fado kansu a kan titi.

Hukumar rage cinkoso ta jihar Legas (LATSMA) ta ce har yanzu ana cigaba da kokarin tsamo wadanda tsautsayin ya ritsa da su.

Ojuelgba
Kwantenar Kaya Ta Rikito Kan Motar Haya a Legas, Mutum 9 Sun Ce Ga Garinku Hoto: @thecable
Asali: Facebook

Sakataren hukumar agaji na gaggawa na jihar Legas (LASEMA), Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ta ce mutum tara ne suka mutu kawo yanzu - biyu cikinsu yara ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Saura ranar aiki 1 kacal, CBN Tace Ta Fitar Da Sabbin Kudi N120m Jihar Katsina

A cewarta:

"Yayinda muka isa wajen, wata babbar mota dauke da kwantenar 20ft ta rikito kan wata motar haya Bas."
"Karin bincike ya nuna cewa Bas din na daukan fasinja yayinda babbar motar ta kwacewa direban kuma ya rikito daga kan gada."
"Bayan cire kwantenan da injin hukumar, mutum daya wata mata ta tsallake rijiya da baya kuma an kaita cibiyar kula."
Kwantena
Kwantenar Kaya Ta Rikito Kan Motar Haya a Legas, Mutum 9 Sun Ce Ga Garinku Hoto: @followlatsma
Asali: Twitter

Wani mai idon shaida ya bayyana a shafin Tuwita kanar yadda @PoojaMedia ta daura cewa hadarin ya auku ne sanadiyar kokarin babbar motar na hana Bas din wuceta.

A cewae jawabin:

"Yanzu kwantena ya fadi kan Bas a gadar Ojuelegba. Akwai mutane ciki dam."

Wani mai idon shaida, (direban Uber) ya ce direban babbar motan na kokarin hana Bas din wuceshi.

Labarin hadarin jirgin kasa Abuja/Kaduna

Kun ji labarin cewa watanni biyu kacal bayan dawowan aikin jirgin kasan Abuja/Kaduna, jirgin ya gamu da hadari inda ya kauce daga kan hanya yana gab da shiga Abuja.

Kara karanta wannan

Amarya Ta Antayawa Uwarginta Tafasashen Ruwa Kan Zargin Maita A Jihar Kwara

Wadanda suka shaida abin sun ce barayin karafa ne suka kwance layin dogon kma haka yayi sanadiyar hadarin.

Dadin abin babu wanda yaji rauni ko rashin rai.

Hukumar jiragen kasan Najeriya NRC ta dakatar da tafiyar jirgin yanzu gaba daya sai ila maa shaa'aLLLAHu.

Wannan na faruwa ne yan kwanaki bayan hadarin jirgin Warri/Itapke dake jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida