Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hadari Kusa Da Kubwa Abuja

Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hadari Kusa Da Kubwa Abuja

Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya yi hadari a unguwar Kubwa yayinda yake gab da isa manufarsa.

ZagaZola Makama ya bayyana cewa wannan abu ya faru ne da yammacin nan kusa da manufarsa dake unguwar Kubwa Abuja.

A cewarsa, babu wanda aka rasa ko ya samu rauni a hadarin.

A cewarsa:

"Jirgin kasa daga Kaduna ya yi hadari da yammacin nan kusa da tashar Kubwa Abuja saboda barayi karafe sun kwance titin. Dukkan fasinjoji na nan cikin koshin lafiya."

Kalli hotunan:

Jirgi
Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hadari Kusa Da Kubwa Abuja Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgi
Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hadari Kusa Da Kubwa Abuja
Asali: Twitter

Jirgi
Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hadari Kusa Da Kubwa Abuja Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

jirgi
Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hadari Kusa Da Kubwa Abuja
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel