Hoton Gwamna Sule Yayin da Yake Yi Wa Gawar Dansa Addu’a Kafin a Sada Shi Da Gidansa Na Gaskiya

Hoton Gwamna Sule Yayin da Yake Yi Wa Gawar Dansa Addu’a Kafin a Sada Shi Da Gidansa Na Gaskiya

  • Zukata sun yi nauyi bayan bayyanar hoton Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa yana yi wa gawar dansa na fari addu'a
  • Gwamnan ya rasa babban dansa, Hassan Sule a ranar Juma'a bayan ya yi fama da rashin lafiya a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa
  • Wani dan Najeriya mai suna Ayoola wanda ya bayyana cewa jarabtan Allah ya fi dukiya da matsayinmu shine ya saki hoton

Nasarawa - An gano hoton gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, wanda ke jimamin rashi da ya yi a gaban gawar dansa, Hassan Sule yana yi masa addu'a.

An tattaro cewa Hassan Sule ya rasu ne a safiyar ranar Juma'a, 27 ga watan Janairu bayan yar gajeruwar rashin lafiya a garin Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

Gwamna Sule da gawar dansa
Hoton Gwamna Sule Yayin da Yake Yi Wa Gawar Dansa Addu’a Kafin a Sada Shi Da Gidansa Na Gaskiya Hoto: Twitter/@AYOOOLA007
Asali: Twitter

Gwamna Sule yana yi wa gawar dansa addu'a

Wani mai alhinin mutuwar, @AYOOOLA007, ya garzaya shafinsa na Twitter don wallafa hoton lokacin da yake yi wa dan nasa addu'a sannan ya roki Allah ya ba iyalin mamacin dangana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Wannan gwamna ne mai ci yake yi wa gawar babban dansa addu'a. Jarabtan Allah ya fi karfin kudi da matsayin mutum."

Kalli wallafa a kasa:

An tattaro cewa Hassan ya rasu yana da cewaru 36 a duniya.

Jama'a sun yi martani

Wasu yan Najeriya sun garzaya sashin sharhi domin yi wa gwamnan da ahlinsa ta'aziyya.

@naijateddy ya ce:

"Allah ubangiji ya karfafa shi sannan ya ba iyalin dangana. Babu uban da ya cancanci binne dansa. Kamata ya yi abun ya zama akasin haka."

@hafidaibrah ta ce:

"Allah ya gafarta masa ya kuma ji kan mamacin, Allah SWT ya ba masoyansa hakuri sannan ya basu juriyar wannan rashi, aameen."

Paul Ikenna Esq. ya ce:

"Wannan hoton na daya daga cikin mafi tsuma zuciya da na taba gani."

Toyin. SM. Adeyemi ta yi wa iyalin addu'a:

"Ya Ubangiji ka ji kansa...ka ba mahaifinan da ahlinsa hakuri. Iyaye basu cancanci fuskantar irin haka ba. Ina mai mika ta'aziyyata. Ina mai baka hakurin wannan rashi."

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Edo zata fara rufe masallatai da cocina da sauran wurare idan har basu dauki matakin hana fitar sauti daga gine-ginensu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel