Zargin Zagon Kasa: ISWAP ta Fatattaki Mayakan Boko Haram da Suka Musu Mubaya'a

Zargin Zagon Kasa: ISWAP ta Fatattaki Mayakan Boko Haram da Suka Musu Mubaya'a

  • Shugaban kungiyar ta'addanci ta ISWAP, Abba Shuwa, ya bukaci tsofaffin mayakan Boko Haram da ke cikinsu da su mika makamansu tare da kama gabansu
  • Ya alakanta nasarorin da dakarun sojin Najeriya ke samu a kansu da cin amana, zagon kasa da fuska biyu da wasu mayakan ke yi inda suke kai bayanan sirri
  • Yace har yanzu ba mubaya'ar gaskiya suka yi ba, zukatansu na tare da shugaban Boko Haram Abou Oumymah

Borno - ‘Yan ta’addan kungiyar ISWAP sun kori tsofaffin mambobin Boko Haram da suka koma kungiyar tare da mubaya’a ga ISWAP bayan mutuwar Shekau.

Taswirar Borno
Zargin Zagon Kasa: ISWAP ta Fatattaki Mayakan Boko Haram da Suka Musu Mubaya'a. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Abubakar Shekau, tsohon shugaban kungiyar Boko Haram, ya halaka kansa yayin wata arangama tsakaninsa da manyan kwamandojin ISWAP a watan Yunin 2021.

Makonni bayan mutuwarsa, dubban mambobin Boko Haram sun yi mubaya’a ga Aba Ibrahim Al-Hashimiyil AlKhuraishi wanda kai tsaye aka nada shi Khalifan Musulmai.

Kara karanta wannan

Canjin Kudi: Kwankwaso Ya Yi Alkwarin Gyara ‘Kuskuren’ da Aka Yi Idan Ya Ci Zabe

Wata majiyar sirri ta sanar da Zagazola Makama cewa, watanni 19 bayan hade shugabancin ISWAP da Boko Haram an sanar da ‘yan Boko Haram cewa lokaci yayi da zasu bar kungiyar saboda zargin wasu daga ciki ‘yan leken asiri ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsanantar yakarsu da dakarun sojin Najeriya ke yi tayi sanadin mutuwar daruruwan ‘yan ta’addan da tarwatsewar maboyarsu a watannin da suka gabata.

Majiyoyin sun ce tsagin ISWAP na cigaba da hasashen cewa nasarar da sojin Najeriya ke samu a kansu ba ta wasa bace, lamarin da yasa suka zargi da hadin bakin wasu daga cikinsu.

Sun ayyana cewa, rikicin kungiyoyin da arangamar da ake ta yi tsakanin Bakoura Doro wanda aka fi sani da Abou Oumaymah na Boko Haram da kungiyar ISWAP din ke kawo nasarar a kansu.

Yayin jawabi ga mayakan da iyalansu a Timbuktu, shugaban ISWAP, Abban Shuwa wanda aka fi sani da Ba’a Shuwa, ya zargi mayakan Boko Haram da fuska biyu.

Kara karanta wannan

Kamfe Ya Tsaya Babu Shiri Bayan An Kora ‘Yar Takarar M/Gwamna da Ta je Yakin zabe

Yace:

“Za ku iya ikirarin cewa ku sojojin Khalifah ne amma zukatanku suna tare da Murtad da Khawarij. Har yanzu kuna biyayya ga tsagin Abubakar Shekau.
“Har yau goyon bayan Abou Oumaymah da Ali Ngulde ku ke.”

Shuwa ya zargi mayakan Boko Haram da hada kai da tubabbun ‘yan Boko Haram wurin fallasa tsare-tsarensu na hari wanda hakan ke kawo musu rashin nasara.

Ya nada misalin ranakun 14 da 23 ga Janairun 2023, hare-haren da suka kawo ajalin ‘yan ta’adda masu yawa da kwace makamansu da dakarun sojin Najeriya suka yi a Damboa.

A don haka, ya shawarci mayakan Boko Haram din da su mika makamansu tare da barin kungiyar ko su fuskanci fushinsa.

Mahaka ma'adanai 5 sun mutu bayan harin 'yan bindiga

A wani labari na daban, miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki kan masu hakar ma'adanai a Udawa da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Sun yi nasarar halaka mutane biyar a wurin wanda shugaban yankin ya tabbatar da faruwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel