First Bank da GT Sun Amince Zasu Yi Aiki A Karshen Mako Don Karban Tsaffin Kudi

First Bank da GT Sun Amince Zasu Yi Aiki A Karshen Mako Don Karban Tsaffin Kudi

  • A ranar 31 ga watan Janairu, 2023 nan da kwanaki kaɗan tsoffin takardun N200, N500 da N1000 zasu daina amfani
  • Babban bankin Najeriya ya kafe kan wa'adin da ya sa duk da matsin lambar da yake sha daga masu ruwa da tsaki
  • Sai dai Bankunan First Bank da GT sun fitar da sanarwa kan matakin da suka ɗauka domin kar yan Najeriya su yi asara

Bankuna guda biyu, First Bank Nigeria da kuma Guaranty Trust Bank sun sanar da cewa rassansu dake faɗin ƙasar nan zasu fito aiki a ranakun ƙarshen mako, Asabar da Lahadi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa zasu buɗe bankuna ne domin karban tsoffin takardun Naira yayin da wa'adin babban banki CBN ke ƙarewa ranar 31 ga watan Janairu, 2023.

Kara karanta wannan

Ta Kacame: APC Ta Fatattaki Wani Ministan Buhari Daga Jam'iyya? Gaskiya Ta Bayyana

Tsoffin kuɗi a Najeriya.
First Bank da GT Sun Amince Zasu Yi Aiki A Karshen Mako Don Karban Tsaffin Kudi Hoto: dailytrust
Asali: Depositphotos

A wata sanarwa da mahukuntan bankunan suka fitar ranar Jumu'a, sun bayyana cewa sun tsara aiki a karshen mako ne don mutane su samu damar shigar da tsoffin kuɗinsu kaɗai.

"Muna sanar da ɗaukacin 'yan Najeriya cewa rassunan mu zasu fito aiki ranar Asabar da Lahadi domin su karɓi tsabar kuɗi kaɗai."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dukkan tsoffin takardun kuɗi N200, N500, da N1000 zasu daina amfani daga ranar 31 ga watan Janairu, 2023," inji Bankin First Bank a sanarwan da ya fitar.

Babban bankin Najeriya (CBN) ya jaddada cewa ba gudu ba ja da baya tsofaffin takardun kudi N200, N500, da N1000 zasu daina amfani daga ranar 31 ga watan Janairu, 2023, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa wa'adin na nan daram duk da matsin lambar da babban bankin ke sha daga masu ruwa da tsaki ta kowane fanni na ya kara wa'adin.

Kara karanta wannan

Baku isa ba ku karya kasa: Majalisa ta dura kan CBN game da sabbin Naira, ta fadi matakin da za ta dauka

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa 'yan Najeriya na fama da rashin yawaitar sabbin kuɗi yayin da wasu wuraren da yan kasuwa suka rufe shagunansu saboda basu karban tsaffi.

Sabbin Kudi sun rage yawan sace mutane da neman kuɗin fansa, CBN

A wani labarin kuma Gwamnan CBN ya bayyana babbar illar da yake tunanin sauya takardun kudi ya yi wa yan bindiga

Godwin Emefiele yace mai yuwawa sabon tsarin ya rage wa yan ta'adda karfin karɓan kudin fansa saboda ba'a amsar tsoffi.

Emefiele ya jaddada cewa ba gudu ba ja baya game da karewar wa'adin tsoffin takardun N200, N500 da N1,000 ranar 31 ga watan Janairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel