Sabon Matsala Ga Atiku Yayin Da Kotu Ta Amince A Dauki Muhimmin Mataki Kan Dan Takarar Na PDP

Sabon Matsala Ga Atiku Yayin Da Kotu Ta Amince A Dauki Muhimmin Mataki Kan Dan Takarar Na PDP

  • Wata babban kotun tarayya da ke Abuja ta bada izinin a mika takardun kotu ga Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023
  • Umurnin da aka bada ya umurci a mika takardun shigar da kara kansa ta hannun kungiyar yakin neman zabe na Atiku Abubakar
  • Festus Keyamo, mai magana da yawun kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC, a baya ya nemi a fara yin shari'ar ko da wanda ake karar bai bayyana a kotu ba

FCT, Abuja - Wata babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bada umurnin a mika takardun kotu kan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Atiku Abubakar, kan tuhuma mai alaka da almundahar kudi.

A cewar Daily Trust, kotun ta bada umurni cewa a mika takardun ta hannun kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na Atiku Abubakar da ke Ademola Adetokunbo Crescent, Wuse II, a Abuja.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu Ya San Cewa Atiku Ne Zai Zama Shugaban Kasa, In Ji Shu'aibu

Atiku Abubakar
Sabon Matsala Ga Atiku Yayin Da Kotu Ta Amince A Dauki Muhimmin Mataki Kan Dan Takarar Na PDP. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

An bada wannan umurnin ne sakamakon wani kara da Festus Keyamo, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC ta hannun lauyansa, John Ainetor kuma ya tura wa Atiku takardun kotun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ke faruwa a baya-bayan nan game da Atiku Abubakar, PDP, Festus Keyamo, Zaben 2023, Babban Kotu

A ranar Juma'a, 20 ga watan Janairu, Keyamo ya rubuta korafi yana bukatar kotun ta umurci Atiku ya bawa hukumomin yaki da rashawa bayanai na wani asusun banki mallakar wani kamfani mai suna Marine Float, da wasu kamfanonin 2 da ba a bayyana ba amma aka kira su da suna Special Services Vehicles, (SPVs).

An yi zargin cewa an yi amfani da kamfanonin don karkatar da kudade a lokacin da Atiku ke mataimakin shugaban kasa tsakanin 1999 zuwa 2007.

Kara karanta wannan

Tinubu bai zagi Buhari ba, PDP da wasu yan jarida ke kokarin hada su rigima: Inji APC

Hukumomin yaki da rashawar da aka lissafa sun hada da Hukumar yaki da rashawa da wasu laifuka masu alaka, (ICPC), Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, (EFCC), da kotun da'ar ma'aikata wato (CCB).

Asali: Legit.ng

Online view pixel