Sabbin Kudi sun rage yawan sace mutane da neman kuɗin fansa, CBN

Sabbin Kudi sun rage yawan sace mutane da neman kuɗin fansa, CBN

  • Gwamnan CBN ya ce a tunaninsa sauya takardun naira ya taimaka wajen rage aikata manyan laifukan garkuwa
  • Godwin Emefiele yace mai yuwawa sabon tsarin ya rage wa yan ta'adda karfin karɓan kudin fansa saboda ba'a amsar tsoffi
  • Yace babban bankin ƙasa bai manta da mutanen karkara da masu karamin karfi kuma zai neme su ko da bayan karewar wa'adi

Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, yace sabbin takardun kuɗin da aka sauya sun rage yawan garkuwa da mutane da karɓan kuɗin fansa.

Gwamnan ya yi wannan ikirarin ne yayin da yake jawabi bayan taron kwamitin tsara takardun naira na bankim CBN a babban birnin tarayya Abuja ranar Talata.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Sabbin Kudi sun rage yawan sace mutane da neman kuɗin fansa, CBN Hoto: channelstv
Asali: Getty Images

Channels tv tace a yayin wannan jawabi ne Emefiele ya jaddada cewa ba gudu ba ja baya game da karewar wa'adin tsoffin takardun N200, N500 da N1,000 ranar 31 ga watan Janairu, 2023.

Kara karanta wannan

Wa'adin tsaffin Naira: Kananan hukumomi 4 Kacal ke da banki jihar Yobe, Mai Mala ya koka

"Magana ta gaskiya, a ɗan wannan lokacin, zata iya yuwuwa ba haka bane amma a tunani na garkuwa da mutane da kuma neman kudin fansa sun ɗan ragu ta wani fannin. Jami'an tsaro sun kara zage dantse."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina ganin (sauya takardun naira) ya sa mutanen nan sun ja baya saboda sun san idan suka karbi tsaffin kuɗi ba zasu amfane su ba. Tunani na zai iya zama haka ne zata iya yuwuwa kuma ba haka bane."

- Godwin Emefiele.

Gwamnan ya kara da bayanin cewa CBN na sane da mutane masu karamin karfi da yan kauye kuma bankin zai je har inda suke don tabbatar da sun samu sabbin takardun.

Bayan haka, Gwamna Emefiele ya sanar da ƙara kuɗin riba MPR daga kashi 16.5% zuwa kaso 17.5% da nufin dakile hauhawar farashi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: CBN ya kawo mafita ga mutanen kauye, ya kawo wani sabon tsari mai kyau

A cewar Godwin Emefiele ba bu ɗan Najeriya fa aka ba shi lasisin gima wurin ajiyar kuɗaɗe a cikin gidansa.

Kananan Hukumomi 4 Kacal Ke da Banki a Jihar Yobe, Mai Mala ya koka

A wani labarin kuma Gwamna Mala Buni na jihar Yobe ya roki babban bankin Najeriya ya kara wa'adin karɓan tsaffin kuɗi

A wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan kan al'umaran sadarwa, Mamman Muhammed, ya fitar, Buni ya koka cewa babu isassun bankuna a jihar Yobe.

Sanarwar tayi bayani cewa a kananan hukumomin sha 17 da ke Jihar Yobe, guda hudu ne kawai suke da bankunan kasuwanci a jihar, kuma hakan zai wahalar da yan Yoben su samu damar canja kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel