Ba Za Mu Bar CBN Ya Jefa Tattalin Arzikin Kasa Cikin Hadari Ba, in Ji Majalisar Wakilai

Ba Za Mu Bar CBN Ya Jefa Tattalin Arzikin Kasa Cikin Hadari Ba, in Ji Majalisar Wakilai

  • Majalisar kasa ta bayyana bukatar ganin shugabannin Babban Bankin Najeriya (CBN) don warware wasu batutuwa game da sabbin Naira
  • Wannan na zuwa bayan da ‘yan Najeriya suka fara nuna damuwa game da mayar da tsoffin kudade tare da wahalar samun sabbi
  • Majalisar ta ce ba za ta bari wasu daidaikun mutane su lalata tattalin arzikin kasar nan ba, ta fadi abin da za ta yi a kai

FCT, AbujaMajalisar wakilai ta kasa ta ce ba za ta bari Babban Bankin Najeriya (CBN) ya jefa kasar cikin mawuyacin halin tattalin arziki ba.

Majalisar ta fahimci cewa, matukar aka bi batun CBN na haramta amfani da tsoffin kudi nan 31 ga watan Janairu, to hakan zai shafi tattalin arziki.

Shugaban kwamitin wucin gadi kan harkokin kudi, Hassan Ado-Doguwa ya ce, an gayyaci jami’an CBN zuwa majalisar amma sun gaza zuwa.

Kara karanta wannan

Mafita: Dan gwamnan PDP ya rasu, INEC ta fadi yadda za a maye gurbinsa

Majalisa ba za ta bari a bata tattalin arzikin kasa ba
Ba Za Mu Bar CBN Ya Jefa Tattalin Arzikin Kasa Cikin Hadari Ba, in Ji Majalisar Wakilai | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A cewarsa, ya zama dole majalisar ta zauna da jami’an CBN a yau Alhamis 26 ga watan Janairu da misalin karfe 1 na rana, rahoton The Nation.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ba za a karya tattalin arzikinmu ba

Da yake jawabi game da tsarin CBN na daina amfani da tsoffin N200, N500 da N1,000 nan da karshen wata, dan majalisar ya ce:

“Ba za mu jefa tattalin arzikinmu cikin hadari ba. Ba kuma zamu bari wani jefa tattalin arzikinmu cikin hadari ba.”

Ya kuma bayyana cewa, wannan lamari ya shafi tattalin arzikin kasa, kuma ya shafi muradin ‘yan Najeriya don haka dole a dauki mataki, rahoton TheCable.

Lamarin nan ya shafi al’ummarmu

Ya kara da cewa:

“Ya shafi dogewar tattalin arzikinmu. Ya shafi al’ummarmu.
“Ana ta dakatar da harkokin kasuwaci ta ko’ina. Harkar noma na shan wahala. Kananan kasuwanni a kauyuka na shan wahala.

Kara karanta wannan

Mai Dakin Tinubu Za a Damkawa Mulki Idan Har Aka Zabi APC - Naja’atu Muhammad

“Na ji a wasu wuraren har sadaki ma an an kir karba na tsohon kudi, Don haka, wannan ba karamin lamari bane.”

Hakazalika, Ado-Doguwa ya ce aikin majalisa ne ta tuhumi kowace hukuma da jami’an gwamnati a madadin al’ummar kasa, don haka za ta ji bahasi daga babban bankin.

Babban abin da ya fi damun ‘yan Najeriya a halin yanzu shine yadda sabbin kudade za su wadata a bankunan kasar, kuma su iya shigar da tsoffi ba tare da tangarda ba.

CBN ya dage kan matsayarsa, ya ce babu laifinsa a karancin kudi, bankuna ne suka ki zuwa daukar kudade.

Asali: Legit.ng

Online view pixel