Dattawan Arewa Sun Yi Gargadin Kan Shirin Yin Katsalandan A Zaben 2023

Dattawan Arewa Sun Yi Gargadin Kan Shirin Yin Katsalandan A Zaben 2023

  • Dattawan yankin arewacin Najeriya sun yi magana da kakkausan murya a yayin da ake fuskantar babban zaben 2023 game da yiwuwar rashin yin zabe
  • Dattawan karkashin kungiyarsu ta NEF sun gargadi wasu da suka ce suna shirin kawo katsalandan ga zaben shekarar 2023 da su shiga taitayinsu
  • NEF, ta bakin mai magana da yawunta Dr Hakeem Baba Ahmed ta ce kasar ba za ta amince da wani tsari da baya cikin kundin tsarin mulki ba

Kungiyar Dattawan Arewa, NEF, ta gargadi wasu mutane da ke shirin yin katsalandan kan zabe da mika mulki ga sabuwar gwamnati cikin lumaba su shiga taitayinsu, rahoton Daily Trust.

NEF ta ce ta yi nazarin mawuyacin halin da yan arewa da sauran yan Najeriya ke rayuwa a yanzu, da kuma damuwa da ake kan tsaro yayin zaben da za a yi a watan Fabarairu da Maris din wannan shekarar.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Kai Ziyarar Bazata Kudancin Borno, Ya Kafa Tarihi

Hakeem Baba Ahmed
Dattawan Arewa Sun Yi Gargadin Kan Shirin Yin Katsalandan A Zaben 2023. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun direktan watsa labarai na kungiyar, Dr Hakeem Baba-Ahmed, Dattawan sun ce akwai kananan maganganun cewa ba za a yi zabe ba, kuma za a kakkabawa yan Najeriya wani tsari wanda ba bisa kan zabe ba bayan Maris din wannan shekarar.

NEF ta ce wadanda ke yada jita-jitan na nuni ga mawuyacin halin da yan Najeriya ke rayuwa a yanzu.

Sanarwar ta ce:

"Suna cewa wahalhalun da rashin tsaro, tsadar rayuwa, karancin man fetur, sauya tsaffin kudi don sabbi da wasu abubuwa za su shafi talakawan Najeriya kuma da gangan suna son tunzura su don kawo matsala ga zabe ko barazanar rashin yin zaben.
"Kungiyar ta ce babu dalilin da zai sa ta goyi bayan hakan. Kuma ta gargadi duk wasu masu nufin kawo cikas ga sahihin zaben da mika mulki ga sabuwar gwamnati cikin lumana.

Kara karanta wannan

An Haramtawa Wasu ‘Yan Najeriya Shiga Amurka, Atiku Ya Yi Maza Ya Yi Magana

"Tabbas matsain tattalin arziki da wahalhalun da yan Najeriya ke fuskanta barazana ne ga zaman lafiya da tsaro. Dole a nemi hanyar inganta tsaron mutane da kasa. Dole a kawar da karancin man fetur baki daya."

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"Tsarin sauya kudi bai tafi yadda aka shirya ba, kuma yana kawo cikas ga kasuwanci tare da jefa mutane cikin matsi. A sake duba abin, musamman wa'adi da yadda CBN da sauran bankuna ke aiki.
"Duk wani amfani da ya ke da shi, ba zai zama mai alfano ba idan ya lalata tattalin arziki, ko ya jefa talakawa cikin wahala. Kungiyar ta bada shawara a dage ranar dena karbar tsaffin kudin da cigaba da zaman shugaban na CBN kan kujerarsa.
"Kungiyar ta yi gargadin cewa yan Najeriya ba za su zauna ba a cikin wani tsari da ya ci karo da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya."

NEF ta bayyana sharadin goyon bayan dan takarar shugaban kasa a 2023

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Gwamnan CBN ya ki zuwa majalisa kan batun sabbin Naira, kakaki ya fadi matakin da zai dauka

A baya, rahoto ya zo inda kuka ji cewa kungiyar ta NEF ta bayyana sharruda kan mara wa wani dan takarar shugaban kasa baya a zaben 2023.

Dr Hakeem Baba-Ahmed, kakakin NEF ya ce a wannan karon dattawan ba za su nanata kuskuren da suka yi wurin goyon bayan Shugaba Buhari ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel