Hankalin Ango ya Tashi Bayan Wani ya Mikawa Amarya Karamar Takarda Wurin Biki

Hankalin Ango ya Tashi Bayan Wani ya Mikawa Amarya Karamar Takarda Wurin Biki

  • Ranar bikin wata amarya ya haskaka yayin da wani mutumi kwatsam ya mika mata wasikar taya murnar aurenta yayin da ake tsaka da shagalin bikin
  • A lokacin da yayi arba da takardar hannun amaryarsa, angon ya nuna damuwa karara har sai da ya karanta abun da takardar ke dauke da shi
  • Mutane da dama da suka yi martani mai ban dariya kan bidiyon sun ce alamu na nuna wasikar tazo ne daga tsohon sauranyinta

Wani matashi, mai amfani da @thedaveblog, wanda ya saba kirkirar maudu'i ga baki don jin ta bakinsu ya sake maimaita irin haka ga wata kyakkyawar amarya ranar aurenta.

Ango da amarya
Hankalin Ango ya Tashi Bayan Wani ya Mikawa Amarya Karamar Takarda Wurin Biki. Hoto daga TikTok/@thedaveblog
Asali: UGC

A wani faifan bidiyon TikTok, an ga wata amarya zaune kusa da angonta yayin da ya miko takardar zuwa gareta.

Ta hade rai yayin da ta yi kokarin bude takarda. Haka zalika, shima angon ya nuna damuwa karara a fuskarsa. Bayan karanta takardar, matar ta murmusa.

Kara karanta wannan

Uwa Ta Koka, Ta Saki Takarda Da Hoto Da Ta Gani a Jakar Makarantar Diyarta Mai Shekara 10, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Mijin nata da ya leka takardar shi ma ya yi kokarin yin murmushi. Takardar ta nuna:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ina miki fatan alheri a rayuwar aurenku."

Mutane da dama da suka kalli bidiyon sun ce angon ya yi ta sake-saken abubuwa da dama a ransa kafin karanta takardar.

Daga lokacin da aka tattara wannan rahoton, bidiyon ya tattara kusan tsokaci 500 da dama da jinjina 300,000.

Martanin jama'a

Legit.ng sun tattaro wasu daga cikin martanin kamar haka:

SPOKEN-REX ya ce:

"Mutumin ya firgita fa."

Big bad E ya ce:

"Mutum ya fito da sirrinsa waje."

Glam_by_Zamdoll ta ce:

"Ina iya jin karar bugun zuciyar mutumin."

Precious ta ce:

"Mutumin ya ji tsoro faaaa."

sherri_dina ya ce:

"Mutumin fa ya gama tsorata."

user81296951494 ya ce:

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Mabarata Sun Dire Gefe, Sun Daina Karbar Tsofaffin Takardun Naira

"Ina son rigar aurenku, Ubangiji ya albarkaci telan da auren naku."

user9874217042055 ya yi zolaya:

"Mutumin ya so sume wa."

21_Savage ya ce:

"Da farko mutumin ya yi tunanin wani abu ne daban sai bayan ta nuna masa takardar. Ubangiji ya albarkaci gidan aurenku."

user382398023014 ya ce:

"Ba zai wuce tsohon sauranyinta ba... Ta san rubutun waye."

Kwadayi ya ja min nadama, Matashi yayi bayani a bidiyo

A wani labari na daban, wani matashi 'dan Najeriya yayi nadamar abinda kwadayi ya ja masa a bidiyon da ya saki a TikTok.

Yace stsabar son kudinsa ya ja masa yake dab da mutuwa, ya bukaci jama'a da su taimaka masa da addu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel