Uwa Ta Saki Takarda Da Hoto Da Ta Gani a Jakar Makarantar Diyarta

Uwa Ta Saki Takarda Da Hoto Da Ta Gani a Jakar Makarantar Diyarta

  • Wata mata ta nuna bakin ciki bayan ta ci karo da wani abu da bata yi tsammani ba a jakar makarantar diyarta
  • Ta cika da mamakin ne irin wannan hoto da wasikar soyayya ke yi a jakar diyar tata wacce shekarunta 10 kacal
  • An yi cece-kuce kan abun da ke rubuce cikin wasikar da hoton yayin mutane da dama suka yi martani mai ban dariya a kansu

Wata mata ta haddasa cece-kuce a shafin soshiyal midiya bayan ta bayyana abun da ta gano a cikin jakar makarantar diyarta karama.

A wata wallafa da ta yi a TikTok, ta wallafa hotunan wasikar soyayya da hoton wani karamin yaro da ta samu a jakar yarinyar kuma ta bayyana cewa zuciyarta ta karaya.

Uwa da wasika da hoton yaro
Zuciyata Ta Karaya: Uwa Ta Saki Takarda Da Hoto Da Ta Gani a Jakar Makarantar Diyarta Hoto: TikTok/@ginger_wenu
Asali: UGC

A wasikar soyayyan, marubucin yana so yarinyar ta gane cewa yana sonta sannan ya nemi sanin ko itama tana jin yadda yake ji game da ita.

Kara karanta wannan

“Wa Ya Shirya Aurena”: Baturiya Ta Yi Alkawarin Bayar Da Kyautar Biza Ga Duk Mutumin Da Ya Shirya Aurenta

Masoyin nata ya kuma bayyana cewa dole ta kasance cikin farin ciki sannan ya kare zantukansa da jaddada soyayyarsa a gareta. Hoton da ke jikin wasikar ya kasance na wani karamin yaro a kan keke.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani

gloMat ta ce:

"Shekarar dana 9 a bara kuma ya rubuta wata wasikar soyayya zuwa ga yar shekara 16 yana fada mata cewa zai daina sonta idan ta ci gaba da ganin saurayinta."

user7284937617867 ya ce:

"Ina mai yi maki maraba da zuwa matsayin uwa nawa shekararta 9 wata rana ta dawo daga makaranta cike da farin ciki inda ta fada mani cewa tana da saurayi."

flo_blossom ya ce:

"Lol kada ki karaya uwa maimakon haka wannan ne damarki da za ki sa ta bude baki ta maki magana ki bata wannan damar.

Kara karanta wannan

“Sharadi Ba Za Ka Yi Mun Kishiya Ba”: Budurwa Ta Yi Alkawarin Baiwa Duk Wanda Ya Aureta Gida, Mota da Miliyan 50 a Bidiyo

Frances ta ce:

"Yho, tawa ta dawo gida ne da kudin da yaron ya bata kuma shekararta 9. Ta samu R20 ko fiye da haka a kullun. Daga baya yaron ya sai mata jan-baki. Ki ji fa!"

Uwa ta shiga damuwa bayan gano wasu abubuwa a jakunkunan yaranta

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata uwa ta shiga damuwa bayan ta gano kudade da abubuwan wasa jibge a jakunkunan makarantar yaranta.

Matar da ta shawarci iyaye su dunga zuba idanu sosai a kan yaransu ta ce suna satar mata kudi suna siyayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel