Bidiyo: Matashi ya Fallasa Yadda Tsabar Son Kudinsa Ya Kai Shi Dab da Ajalinsa

Bidiyo: Matashi ya Fallasa Yadda Tsabar Son Kudinsa Ya Kai Shi Dab da Ajalinsa

  • Wani matashi 'dan Najeriya mai suna Tobeena, ya koka a soshiyal midiya bayan gano cewa sauran kwanaki kadan suka rage ya kwanta dama
  • A wallafar da ya saka a shafinsa na TikTok, ya sanar da cewa idan akwai rayuwa ta gaba, ba zai kara tafka irin wannan kuskuren ba
  • Matashin ya cigaba da shawartar jama'a da kada su saka son kudi ya zama jigon rayuwarsu don yana iya karanta musu kwanakin da zasu yi a duniya

Wani matashi 'dan Najeriya mai amfani da suna @tobenna_billaboy a TikTok ya bada labarin dacin rayuwar da ya shiga bayan tsananin sabo da kudi.

Son kudi
Bidiyo: Matashi ya Fallasa Yadda Tsabar Son Kudinsa Ya Kai Shi Dab da Ajalinsa. Hoto daga @tobenna_billaboy/TikTok
Asali: UGC

A wani sabon bidiyo a TikTok, matashin mai cike da kunar zuciya ya bayyanawa jama'a cewa kwanaki kadan suka rage masa a rayuwarsa.

Kamar yadda yace, tsabar son kudinsa ne ya karanta masa ranakun rayuwarsa, kuma ya shawarci jama;a da kada su bi hanyar da ya bi.

Kara karanta wannan

Ba Zamu Karba Kudin da Zasu Zama Takardun Tsire ba: 'Yan Bindiga Sun ki Karbar Tsofaffin N5.3m na Fansa a Kaduna

Ya cigaba da rokon jama'a da su yi masa addu'a yayin da ya ke cewa ba zai sake tafka irin wannan kuskuren ba a rayuwarsa ta gaba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kada ku bar son kudi ya karanta muku ranakun ku a duniya. Ba zan sake tafka irin kuskuren da nayi ba a rayuwata ta gaba. Kwanaki kadan suka rage in mutu. Zan yi kewar ku. Ku yi min addu'a."

- Yace.

Soshiyal midiya tayi martani

@louisteddy02 tace;

"Da karyayyar zuciya tare da tsananin gaskiya ka nemi yafiyarsa kuma komai zai yi daidai. Ubangijinmu mai rahama ne. Je ka gare shi."

@loveope7 tace;

"Ka yarda da Ubangiji ina tunanin shi ne abinda yafi kyau. Idan ka ga jama'a na magana, tasu suke yi kawai amma ba ka san abinda aka rubuta maka na kaddara ba."

Kara karanta wannan

Ya fasa kwai: Tinubu ya fadi makarkashin yin sabbin Naira da karancin mai a Najeriya

@shalombright77 tace:

"Abun da takaici amma ka san babu abinda yafi karfin kwararre. Kawai ka shaida wanzuwarsa."

@t.wise17 yace;

"Nemi yafiya wurin Ubangiji kuma ka ga malami a yankin ku yayi maka jagora. Tabbas Ubangiji mai rahama ne."

@tabitha595 ta kara da cewa;

"Ubangiji mai rahama ne, yayi wa jama'a masu tarin yawa kuma zai iya yi maka idan ka nemi yafiyarsa."

Baki iya girki ba, na rabu da ke, Matashi ya rabu da budurwa

A wani labari na daban, wani matashi ya fallasa hirarsa da budurwarsa wacce ta kwaba masa girki a karon farko da ta so nuna bajintar ta.

Matashin yace ya rabu da ita kuma ba ya yi saboda bata iya girki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel