Hukumar EFCC Ta Sake Damke Tsohon Shugaban JAMB, Dibu Ojerinde

Hukumar EFCC Ta Sake Damke Tsohon Shugaban JAMB, Dibu Ojerinde

  • Hukumar ICPC ta sake kama tsohon shugaban hukumar shirya jarabawa JAMB, Dibu Ojerinde
  • Bayanai sun nuna cewa an sake kama shi ne bayan wani tsohon Darekta ya ba da shaida a babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja
  • Tsohon Daraktan ya ce Ojerinde ya yi amfani da hi wajen sama da faɗi da kudin gwamnati a hukumar JAMB

Abuja - Jami'an hukumar yaki da masu cin hanci da rashawa da makamantansu (ICPC) sun cafke Dibu Ojerinde, tsohon shugaban hukumar shirya jarabawar shiga jami'o'i (JAMB).

The Cable ta rahoto cewa tsohon mataimakin Daraktan a hukumar JAMB, Jimoh Olabisi, ya shaida wa Kotu cewa tsohon shugaban hukumar ya yi amfani da shi wajen karkatar da kudaden gwamnati.

Dibu Ojerinde.
Hukumar EFCC Ta Sake Damke Tsohon Shugaban JAMB, Dibu Ojerinde Hoto: thecable
Asali: UGC

Mista Olabisi, a matsayin shaidan da hukumar ICPC ta gabatar, ya yi wannan bayanin ne a babbar Kotun tarayya mai zama a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Sai Yanzu Ka San Za Ka Zagi Buhari?, Atiku Ya Caccaki Tinubu

ICPC ta gurfanar da Mista Ojerinde a gaban Kotu ranar 6 ga watan Yuni, 2021 bisa tuhume-tuhume 18 masu alaƙa da zargin sulalewar wasu kuɗaɗe da suka kai Biliyan N5.2bn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta yi zargin cewa tsohon shugaban ya aikata laifukan damfara a lokuta da dama lokacin yana jagorancin JAMB da kuma hukumar shirya jarabawar fita daga Sakandire ta ƙasa (NECO).

Ojerinde ya musanta dukkan tuhumar da ake masa kuma Kotu taba da Belinsa kan kudi miliyan N200m.

Yadda Ojerinde ya yi amfani da ni

Mista Olabisi ya shaida wa Kotu ranar Laraba cewa shi ke kula da kowane Asusu a JAMB kuma ya yi bayanin cewa ya bude wani Asusu da sunan JAMB/J.O. Olabisi bisa umarnin tsohon shugaban.

Ya bayyana wa mai shari'a cewa ta wannan sabon Asusu ne suke ɗibar kudi daga Aljihun gwamnati suna zuba wa a can, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ta Karewa Tinubu a Arewa, Hadimin Gwamna, Sakataren APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Fice Daga Jam'iyar

"Umarnin bude Asusun ya samu sa hannun Ojerinde da daraktan kuɗi na lokacin, Mallam Umar Yakubu, kuma suka ɗora mun kuladm da hada-hadar kuɗi a Asusun," inji shi.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Naɗa Tsohon IGP a Matsayin Shugaban Hukumar PSC

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar shugaban kasa a zaman Sanatocin na ranar Talata, 24 ga watan Janairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262