Hadimin Gwamna, Sakataren APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma NNPP a Gombe

Hadimin Gwamna, Sakataren APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma NNPP a Gombe

  • Wata ɗaya kacal gabanin babba zaben 2023 jam'iyyar APC mai mulki a jihar Gombe ta ƙara shiga matsala
  • Mai ba gwamna shawara, Sakataren APC, hadimin Sanata da wasu shugabanni sun sauya sheka zuwa NNPP
  • Sun ce gwamnati mai ci ta gaza ta fannoni da dama don haka suka koma NNPP su goyi bayan Mailantarki

Gombe - Yayin da zabe ya kusa, jam'iyyar APC mai mulki ta sake samun tasgaro a jihar Gombe yayin da manyan shugabanninta da masu rike da mukaman gwamnati suka sauya sheƙa zuwa NNPP.

Jaridar Tribune ta tattaro cewa kusoshi da mambobin APC a kananan hukumomin Billiri da Shongom sun koma NNPP domin haɗuwa da ɗan takarar gwamna, Khamisu Mailantarki.

NNPP a jihar Gombe.
Hadimin Gwamna, Sakataren APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma NNPP a Gombe Hoto: tribuneonline
Asali: UGC

Daga cikin manyan masu sauya shekar har da Sakataren APC a karamar hukumar Shongom, Nelson Bagudu, da mai ba gwamna shawara ta musamman, Jesse Dereba Maipundi.

Kara karanta wannan

Babbar Matsala Ta Kunno Kai, Jam'iyyar APC Ta Kori Hadimin Shugaban Kasa Buhari Kan Abu 1

Hadimin Sanata mai wakiltar mazaɓar Gombe ta kudu, Mela Lasoru Ibn Lele da Honorabul Alhassan Musa Aliyu suna cikin jiga-jigan da suka koma NNPP domin kwace mulki a hannun APC a 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Vanguard ta rahoto cewa an samu wannan ci gaban ne kwanaki Tara bayan tsohon kwamishinan matasa da wasanni da mamba mai wakiltar Kaltungo sun koma NNPP duk a jihar Gombe.

Meyasa suka yanke shawarar shiga NNPP?

Da yake jawabi a madadin masu sauya sheka, Bagudu ya ce sun yanke ficewa APC ne saboda rashin iya shugabanci da gazawar gwamnati mai ci wajen shawo kan matsalar tsaro da karayar tattalin arzikin da mutane ke fama.

A cewarsa, gwamnatin APC mai ci ba ta da wasu tsaruka da ta sanya a gaba wanda za'a iya cewa zasu tallafawa talakawa su san ana shugabantarsu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Bayan Gazawar APC da PDP, Yan Najeriya Suna da Wani Zabi Ɗaya Rak

Saboda haka ya yi kira a mutane masu hankali da tunani da ke APC da PDP da su sauya tunani su dawo NNNP domin manyan jam'iyyun biyu sun gaza.

Zamu dawo da zaman lafiya - Mailantarki

Da yake maraba da masu sauya shekar, ɗan takarar gwamnan NNPP a Gombe ya ce idan aka zaɓe shi a watan Maris zai dawo da zaman lafiya kuma zai farfaɗo da kananan sana'o'i cikin kwana 100 na farko da kama aiki.

A wani labarin kuma Kwamishina Ya Musanta Rahoton Masari Ya Cire Kusan Miliyan N500m Don Tarban Buhari a Katsina

Wafa wasika da ta bayyana a Soshiyal Midiya ta nuna cewa gwamna Masari ya amince da zare makudan kuɗin domin tara jama'a su tarbi shugaban ƙasa.

Sai dai kwamishinan kananan hukumomin na jihar wanda dole sai da sa hannunsa za'a cire kuɗin ya fito ya yi karin haske kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel