Obasanjo da Fayemi Sun Haɗu da Gwamna Wike a Wurin Taron Ribas

Obasanjo da Fayemi Sun Haɗu da Gwamna Wike a Wurin Taron Ribas

  • Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da tsohon gwamnan Ekiti sun haɗu da gwamna Nyesom Wike a jihar Ribas
  • Obasanjo da Kayode Fayemi sun halarci babban taron Ribas da gwamnatin Wike ta shirya a Patakwal ranar Alhamis
  • Da yake jawabi a wurin, Obasanjo ya bayyana cewa Najeriya ba ta bukatar sake kuskure a zabe mai zuwa

Rivers - Tsohon shugaban kasa, Chief Olusegun Obasanjo, da tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, sun haɗu da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ranar Alhamis 26 ga watan Janairu, 2023.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa manyan mutanen biyu sun haɗu da Wike ne a wurin taron Ribas dake gudana a Patakwal, babban birnin jihar.

Fayemi da Obasanjo da Wike.
Obasanjo da Fayemi Sun Haɗu da Gwamna Wike a Wurin Taron Ribas Hoto: Leardership
Asali: Facebook

Obasamjo da Fayemi sun halarci taron ƙasa da ƙasa na Patakwal 2023 wanda ke gudana a Obi Wali International Conference Centre da ke babban birnin jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Luwadi Ba Laifi Bane: Fafaroma Francis Ya Bayyanawa Duniya

Babban taron na bana an masa take da, "Zurfafa al'adun Demokaraɗiyya domin samun ci gaba da tsaro a Najeriya."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake jawabi a wurin taron, Obasanjo ya ayyana goyon bayansa ga karfafa Al'adun Demokaradiyya, inda ya ƙara da cewa ya zama wajibi yan Najeriya su yi abinda ya dace a zaben wata mai zuwa

Da yake Lakca mai taken, 'Girmama tsarukan demokuradiyya' tsohon shugaban kasan ta ce Demokuradiyyar Najeriya tana kasa tana dabo.

A cewarsa Demokaradiyya ta samu gindin zama a tarihin ƙasar nan ne tun daga lokacin da Sojoji suka miƙa mulki hannun farar hula a shekarar 1999.

Obasanjo ya kara da cewa mai yuwuwa wasu su rika tababa kan darussan da shugabanni da mabiya suka dauka daga tarihin ƙasar nan da kuma rawar da zasu iya takawa wajen ƙara karfafa demokaraɗiyya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Allah Ya Yiwa Limamin Kasar Oyo, Sheikh Mashood Ajokidero III, Rasuwa

APC Ta Fatattaki Wani Ministan Buhari Daga Jam'iyya? Gaskiya Ta Bayyana

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC reshen jihar Akwa Ibom ta musanta wasikar da ke yawo cewa ta dakatar da Ministan harkokin Neja Delta.

Shugaban APC na Akwa Ibom, Stephen Ntukekpo, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana wasiƙar da mashahuriyar ƙarya da wasu tsirarun mutane suka kirkira don jan hankalin al'umma.

Mista Ntukekpo ya ayyana Ministan da cikakken ɗan jam'iyya mai goyon bayan haɗin kan jam'iyyar APC a Akwa Ibom.

Asali: Legit.ng

Online view pixel