Allah Ya Yiwa Limamin Kasar Oyo, Sheikh Mashood Ajokidero III, Rasuwa

Allah Ya Yiwa Limamin Kasar Oyo, Sheikh Mashood Ajokidero III, Rasuwa

  • Babban malamin addini a kasar Yarbawa kuma limamin kasar Oyo ya amsa kiran ubangijinsa
  • Zaku tuna cewa wannan limami ne ya yiwa tsohon Sarkin Oyo da ya mutu salla kwanakin baya
  • Yan uwa da abokan arziki sun yi alhinin marigayi kuma sun yi addu'an Allah ya jikansa da rahama

Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa babban limanin masarautar Oyo, Sheikh Mashood Ajokidero III, ya rigamu gidan gaskiya.

An sanar da mutuwar limamin a shafinsa na Facebook da safiyar Alhamis, 26 ga Junairu, 2023.

A cewar jawabin da aka fitar:

"As salaam alaykum. InnaLillah wainna Ilaihu raajiun. Muna sanar da mutuwar Babban Limamin kasar Oyo. Allah ya bashi Jannatul Firdaos. Amen."

Imam Oyo
Allah Ya Yiwa Limamin Kasar Oyo, Sheikh Mashood Ajokidero III, Rasuwa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Gwamna APC Ya Faɗi Muhimmiyar Maganar da Ya Yi da Gwamnan CBN Kan Sauya Naira

Wani Babban Basarake a Oyo, Abdul-Rasheed Shehu, Ya Rasu

Ɗaya daga cikin sarakunan da ake kira 'Oyomesi', Alapinni na ƙasar Oyo, High Chief Abdul-Rasheed Shehu, ya riga mu gidan gaskiya da safiyar nan ta Lahadi.

Wata majiya daga cikin iyalan gidan Sarautar da suka samu masaniya, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa Sarkin ya rasu ne da safiyar nan bayan fama da wata rashin lafiya da ba'a bayyana ba

Yace za'a masa Jana'iza anjima da yammaci kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada a harabar gidansa.

Idan baku manta ba ɗaya daga cikin 'ya'yan Marigayin mai suna Badira, ta auri Marigayi Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi na III.

Gwamnati ta tabbatar da rasuwar

The Nation tace Gwamnatin ƙaramar hukumar Oyo ta gabas ta tabbatar da rasuwar Basaraken. A sanarwan da ta fitar tace, "Innalillahi wa'inna Ilaihii Raji'uun."

"Cikin raunanannar zuciya da miƙa lamari ga Allah, shugabancin ƙaramar hukumar Oyo ta gabas na bakin cikin sanar da rasuwar Alapinni na Oyoland, Alh Abdul-Rasheed Shehu, da safiyar Lahadin nan 18 ga watan Satumba."

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Na Kasa Ya Fasa Kwai, Ya Ce Zaben Shugaban Kasa Yana da Naƙasu

"Za'a masa jana'iza da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin yau a gidansa, Allah ya jikansa ya sa Aljanna ta zame masa makoma."

Asali: Legit.ng

Online view pixel