Wa’adin Daina Karbar Tsoffin Kudi: Zulum Ya Yi Umurnin Bude Sabbin Bankuna Cikin Gaggawa

Wa’adin Daina Karbar Tsoffin Kudi: Zulum Ya Yi Umurnin Bude Sabbin Bankuna Cikin Gaggawa

  • Yayin da ake ci gaba da kokawa game da matsalar shigar tsoffin kudi banki, Zulum ya samo mafita
  • Gwamnan ya umarci a bude sabbin bankuna a kananan hukumomin jihar don basu damar shugar da tsoffin kudade
  • Gwamnan ya koka da cewa, a yanzu kananan hukumomi biyu ne kacal a jihar ke da bankuna da ke aiki

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, farfesa Babagana Umara Zulum ya umarci wasu ma’aikatun jiharsa masu alaka da kudi da su gaggauta bude sabbin shiyyoyi na bankin Borno Renaissance Mircrofinance a dukkan kananan hukumomin jihar.

Wannan umarni dai ya shafi ma’aikatun kudi, ilimi, kimiyya, fasaha da kirkira, kuma ana bukatar su bude bankunan da cibiyoyin ICT a kananan hukumomi 27 na jihar, rahoton Daily Trust.

Wannan umarni na Zulum na zuwa ne yayin da wa’adin CBN na daina amfani da tsoffin kudi ke karatowa sannan ya gano kananan hukumomi 25 daga 27 na jiharsa basu da bankuna.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Gwamnan CBN ya ki zuwa majalisa kan batun sabbin Naira, kakaki ya fadi matakin da zai dauka

Zulum ya umarci a bude sabbin bankuna a Borno
Wa’adin Daina Karbar Tsoffin Kudi: Zulum Ya Yi Umurnin Bude Sabbin Bankuna Cikin Gaggawa | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Rashin bankuna a yankunan Borno ya samo asali ne daga rikicin Boko Haram na tsawon shekaru 12 da ya dabaibaye yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zulum ya ba da umarnin ne a ranar Laraba 25 ga watan Janairu a birnin Maiduguri yayin wata zama da masu ruwa da tsaki na jihar, ciki har da Shehun Borno, wanda ya samu wakilcin Wazirin Borno.

A bude sabbin bankuna cikin makon nan

Zulum ya ce, kyan samu a kafa sabbin bankuna a yankunan Muguno Gwoza a cikin wannan makon don kaucewa asara daga mutanen kauyuka, DailyPost ta ruwaito.

Da yake magana, Zulum ya koka da cewa:

“A halin da muke ciki muna da bankuna ne a kananan hukumomi biyu kuma su ne Maiduguri da Biu. Tazarar da ke tsakanin wadannan kananan hukumomi yana da nisa sosai.”

Kara karanta wannan

Ba Zamu Karba Kudin da Zasu Zama Takardun Tsire ba: 'Yan Bindiga Sun ki Karbar Tsofaffin N5.3m na Fansa a Kaduna

Ya bayyana cewa, duk da kokarin da aka yi kuma harkar rashin tsaro ta dan lafa a Borno, bankuna sun gaza zuwa don budewa a yankunan.

Dalilin yin wannan hobbasa cikin gaggawa

Saboda haka, gwamnan yace don ya tallafawa mutanensa su samu damar shigar da tsoffin kudade tare da rage musu zafin wahala da suke ciki a yanzu.

Zulum ya kuma umarci ma’aikatar kudi ta jihar da ta kawo hanyar da za ta tabbatar da mutanen kauye sun shigar da tsoffin kudadensu banki nan da 31 ga watan Janairun da ake ciki.

CBN ya ce ba zai daga wa’adin daina amfani da tsoffin kudade ba, domin ya buga wadatattun kudade amma bankuna sun ki zuwa su dauka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel