INEC Ta Umarci a Sake Yin Zaben Fidda Gwanin Gwamna Bayan Mutuwar Dan Takara a Abia

INEC Ta Umarci a Sake Yin Zaben Fidda Gwanin Gwamna Bayan Mutuwar Dan Takara a Abia

  • Ya zama dole jam’iyyar PDP ta sake zaben fidda gwanin gwamna a jihar biyo bayan mutuwar dan takararta na gwamna, Farfesa Uche Ikonne
  • A cewar INEC, jam’iyyar dole ta aske yin zaben fidda gwani nan da kwanaki 14 don maye gurbin mamacin gabanin zaben
  • Kwamishinan hukumar INEC a fannin wayar da kan jama’a, Festus Okoye ya yi karin haske kan abin da hukumar ta tanada

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta umarci jam’iyyar PDP da ta gaggauta sake yin zaben fidda gwanin gwamna a jihar Abia cikin kwanaki 14.

Wannan na zuwa awanni kasa da 24 bayan sanar da mutuwar dan takarar gwamnan jihar a PDP, Farfesa Uche Ikonne a jiya Laraba 25 ga watan Janairu.

Festus Okoye, kwamishinan INEC na kas a fannin wayr da kan jama’a ne ya bayyana cewa, umarnin hukumar ya yi daidai da tanadin sabuwar dokar kundin zabe na 2022, rahoton ThisDay.

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamnan PDP ya rasu, wa zai maye gurbinsa? Ga abin da doka ta tanada

INEC ta umarci a sake zaben fidda gwanin gwamna a Abia
INEC Ta Umarci a Sake Yin Zaben Fidda Gwanin Gwamna Bayan Mutuwar Dan Takara a Abia | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Mataimakin dan takara ba zai maye gurbinsa ba, ga dalili daga INEC

Okoye ya yi karin haske da cewa, sabuwar dokar zabe bata ba da dama ga abokin takara ya maye gurbin mamaci ba kai tsaye kamar yadda wasu suke tsammani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kafa hujja da cewa, wannan kuwa na kunshe a doka ne saboda ba a riga an yi zabe ba balle ya maye gurbinsa a matsayin na’ibi, Punch ta ruwaito.

A cewarsa:

“Shi (mataimakin dan takarar gwamna) ba zai rike tutar jam’iyya idan za a yi zabe. Dole su sake zaben fidda gwani a cikin kwanaki 14 daga mutuwar kana su ba da bahasi ga INEC.”

Okoye ya ce, kwanaki 14 da INEC ta kwasawa PDP sun fara ne daga ranar da dan takarar ya rasu a asibin tarayya d ake babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Saura kiris zabe, dan takarar gwamnan PDP a wata jiha ya kwanta dana

Dan takarar gwamnan PDP a Abia ya rasu

A baya mun kawo muku rahoton yadda aka ba mummunan labarin rasuwar dan takarar gwamnan PDP, Farfesa Uche Ikonne a Abuja.

Dansa ne ya fitar da sanarwa a birnin don bayyanawa duniya cewa, Allah ya yiwa mahaifinsa rasuwa bayan gajeriyar rashin lafiya da ya yi.

A tun farko, an bayyana yadda dan takarar ya yi batan-dabo a wuraren kamfen na PDP duk da kasancewarsa kan gaba a zaben 2023 da ke tafe nan kusa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel