Rudani Yayin da 'Yan Kasuwa Ke Kin Karbar Tsofaffin Takardun Naira a Sokoto

Rudani Yayin da 'Yan Kasuwa Ke Kin Karbar Tsofaffin Takardun Naira a Sokoto

  • Mazauna jihar Sakkwato sun shiga cikin rudani bayan masu saide-saide sun murje ido sun ki amsar tsofaffin kudi
  • Duk da hakan, bankuna na cigaba da bada tsoffin kudi ga kwastomomi da ikirarin basu da sabbi, wanda hakan ya tada hankulan mutane ganin yadda kudadensu ke dab da zama takardun tsire
  • An gano yadda masu shaguna, 'yan acaba da sauran masu kasuwanci suka ki amsar tsofaffin kudin, yayin da wasu suka garkame shagunansu gudun kada a kawo musu kudin da zasu daina aiki a hannunsu

Sokoto - An samu matsanancin rudani a jihar Sakkwato yayin 'yan jihar da dama sukaki amsar tsohon kudi daga kwastomomi.

Tsofaffin Kudi
Rudani Yayin da 'Yan Kasuwa Ke Kin Karbar Tsofaffin Takardun Naira. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Wakilin Punch wanda ya ga yadda lamarin ya auku a fadin jihar ranar Litinin ya tattaro yadda 'yan kasuwa da dama a fadin jihar suka fara kin amsar tsofaffin kudi.

Kara karanta wannan

Akwai matsala fa: Direbobi a wata jihar Arewa sun cije, sun fadi abin da suke so CBN ta yi

Haka zalika, an tattaro yadda 'yan acaba suka ki amsar wannan kudin daga fasinjojinsu.

Yayin zantawa da wakilin Punch, wani mazaunin jihar, Atiku Abdulrafiu, yayi kira ga Babban Bankin Tarayya Najeriya da Gwamnatin Tarayya da su samo mafita don kara wa'adin karbar tsoffin kudi kafin sabbin su yi yawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana yadda a yau, bankuna da dama a jihar suke ba kwastomomi wadannan tsoffin kudin.

"Na je banki yau don cire kudi, mun cire N580,000 amma ka san wani abu? Duk kudin da aka bamu tsoffi ne. Mun bukaci sabbin kudi, amma ga mamakinmu, suka ce basu da sabon kudi.
"Yanzu, taya za ka ji idan 'yan masu saide-saide suka ki karabar wadannan kudin a wannan jihar."

Har ila yau yayin zantawa da wani mai saide-saide a tsohuwar kasuwar Sakkwato, Alhaji Isa Sa'a, ya ce ya yanke shawarar kin bude shagonsa har zuwa karshen watan nan don tsoron amsar tsoffin kudi.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Majalisa za ta kawo mafita, ta fadi abu na farko da za ta yi

A cewarsa:

"Na shaidawa kwastomomina kada su yi yunkurin zuwa shagona sai wani watan saboda ba zan fito kasuwa ba.
"Ba na son amsar kudin da zai daina amfani a gidana."

Sai dai, yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba halin da 'yan Najeriya ke ciki ta kara wa'adin amsar tsoffin kudi don sabbi su yadu.

Bankuna na cigaba da zuba tsofaffin Naira a ATM

A wani labari na daban, bankuna na cigaba da fitar da tsofaffin kudi a injinan bada kudinsu duk da umarnin babban bankin Najeriya da yace su daina zuba su.

Tuni 'yan kasuwa suka koka da yadda sabbin takardun Naira suka yi karanci a hannun jama'a duk da cewa tsofaffin sun kusa zama takardun tsire.

Asali: Legit.ng

Online view pixel