Jirgin Yaki Ya Yi Luguden Wuta Kan Yan Banga a Neja, Da Yawa Sun Mutu

Jirgin Yaki Ya Yi Luguden Wuta Kan Yan Banga a Neja, Da Yawa Sun Mutu

  • Wani jirgin Helikwafta ya yi ajalin Mafarauta dake aikin tsaro da yawa a yankin karamar hukumar Shiroro, jihar Neja
  • Rahotanni sun bayyana cewa ba'a gano jimullan mafarauta nawa lamarin ya halaka ba kuma ba'a san jirgin ba
  • Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Neja ya ce ba zai iya cewa komai ba amma nan ba da daɗewa ba za'a fitar da sanarwa

Niger - Mutane sun shiga yanayin tashin hankali da fargaba bayan wani jirgin sama ya yi ajalin adadi mai yawa na Mafarauta masu aiki da gamayyar jami'an tsaro a Neja.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa harin jirgin ya yi wannan barna ne a Galadima Kogo, karamar hukumar Shiroro, da ke jihar Neja.

Taswirar jihar Neja.
Jirgin Yaki Ya Yi Luguden Wuta Kan Yan Banga a Neja, Da Yawa Sun Mutu Hoto: thenation
Asali: UGC

Rahotanni sun nuna cewa har zuwa yanzun babu cikakken bayani kan jirgin Helkwaftan da ya aikata wannan ɗanyen aiki.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Bayan Gazawar APC da PDP, Yan Najeriya Suna da Wani Zabi Ɗaya Rak

Haka zalika, babu jumullan adadin mutanen da suka rasa rayukansu ciki har da Mafarauta na musamman yayin da ake ci gaba da kokarin gano ɓarnar da lamarin ya haifar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu bayanai sun ce jami'an tsaron, Mafarauta na musamman, waɗanda lamarin ya shafa sun yi sansani ne a garin Galadima Kogo.

Wani mazaunin yankin, Tanko Erena, ya shaida wa jaridar Punch cewa lamarin ya faru ne sakamakon harin jirgin sojin sama lokacin da yan JTF suke sintiri a yankin.

Mutumin ya ce:

"Ina da yakinin na cikin jirgin ya ɗauka mambobin JTF ɗin yan bindigan daji ne saboda babu wani dalili bayan wannan da zai sa haka nan ya jefa masu bam."
"Ba zan iya cewa ga iya adadin gawar da aka ɗauko a wurin ba amma ma ga Motoci biyu da suka ɗauko gawarwakin wadanda suka mutu."

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya saki layin Tinubu? Gaskiya ta fito daga bakinsa, ya bayyana komai

Duk wani kokari na jin ta bakin kwamishinan tsaron cikin gida, Emmanuel Umar, da kuma rundunar yan sanda reshen jihar Neja kan lamarin ya ci tura.

A ɓangarensa, kwamshinan tsaron ya ce ba zai iya cewa komai ba a halin da ake ciki sakamakon yana cikin taron gaggawa amma nan ba da jimawa ba za'a fitar da sanarwa a hukumance.

Yan bindiga sun sace dan bautar ƙasa a Enugu

A wani labarin kuma Miyagun 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane Shida a Jihar Enugu

Wani ganau kuma shugaban wata ƙungiya mai son kawo ci gabaNreshen jihar Enugu , Emeka Odoh, ya ce tsawon kwana uku 'yan bindigan masu rufe fuskokinsu suka kwashe suna addabar mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel