Shugaba Buhari Ya Dura Jihar Legas Don Kaddamar da Sabbin Ayyukan Sanwo-Olu

Shugaba Buhari Ya Dura Jihar Legas Don Kaddamar da Sabbin Ayyukan Sanwo-Olu

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya shilla jihar Legas domin kaddamar da wasu ayyukan da aka yi
  • Gwamna Sanwo-Olu ya yi wasu manyan ayyuka a Legas, ya gayyaci gwamnonin APC da jiga-jigan Najeriya don kaddamar dasu
  • Buhari ya taso ne daga Bauchi, inda aka yi kamfen Tinubu ya wuce Legas don yin wannan babban taro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dura jihar Legas a yau Litinin 23 ga watan Janairu domin kaddamar da wasu ayyuka da Babajide Sanw-Olu ya yi a jiahr.

Ayyukan da Buhari zai kaddamar sun hada da Lekki Deep Sea Port, masarrafar sinkafa ta Imota, layin dogo na Blue Rail da dai sauran ayyuka masu girma da aka yi.

Buhari ya dura jihar ne da misalin karfe 3:33 na yamma, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna Kuma Farfesa Ya Bayyana Mutum Ɗaya Tilo da Zai Iya Ceto Najeriya a 2023

Buhari ya dura Legas kaddamar da wani aiki
Shugaba Buhari Ya Dura Jihar Legas Don Kaddamar da Sabbin Ayyukan Sanwo-Olu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya zuwa yanzu, taron kaddamarwar dai ya samu halartar gwamnan na Legas, Babajide Sanwo-Olu da mataimakinsa Dr. Obafemi Hamzat, Leadership ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, gwamnan Ekiti Biodun Oyebanji da na Ogun Dapo Adiodun duk sun samu halarta.

A bangare guda, shugaban yana tare da tsohon gwamnan Ekiti, Dr. Fayemi Kayode da sauran jiga-jigan gwamnatin jam'iyyar APC a yankin Kudu maso Yamma da ma Najeriya baki daya.

Daga Bauchi ya zarce jihar Legas

Idan baku manta ba, a yau ne shugaba Buhari ya kaddamar da kamfen Bola Ahmad Tinubu da aka yi a jihar Bauchi, Arewa maso Gabashin Najeriya.

Daga jihar ta Bauchi ne ya gangara zuwa jihar Legas domin bude wadannan manyan ayykan da gwamnatin gwamnan APC ta samar.

Shugaba Buhari na ci gaba da yawon tallata dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu da sauran 'yan takarar jam'iyyar a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Shugaban Najeriya Buhari Ya Zauna da Emefiele Bayan Gwamnan CBN Ya Koma Aiki

'Yan shirin fim na Kannywood na goyon bayan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji yadda jaruman fim na masana'antar Kannywood ke kan gaba wajen tallata dan takarar shugaban kasa na APC.

Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ne dan takarar da jam'iyyar su Buhari ta tsayar domin ya zama shugaban kasa a 2023.

Ya zuwa yanzu dai jam'iyyun siyasa na ci gaba da neman goyon baya, suna tallata 'yan takararsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel