Sanatan PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Zolayi Tinubu Kan Barci Da Aka Ce Ya Yi Ta Sharba Yayin Taro

Sanatan PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Zolayi Tinubu Kan Barci Da Aka Ce Ya Yi Ta Sharba Yayin Taro

  • Shehu Sani, tsohon sanata a majalisa zubi ta 8, ya zolayi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, kan ikirarin da aka yi cewa barci ya rika yi yayin taron yan takarar shugaban kasa
  • Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AA, a baya ya yi ikirarin cewa tsohon gwamnan na Legas barci ya rika yi yayin taron da aka yi don tabbatar da yan takarar shugaban kasar sun gudanar da kamfen lafiya
  • A martanin da ya yi kan zargin, jigon na PDP ya bayyana cewa rufe ido baya nufin barci ko gyangyadi ake, ta yi wu addu'a mutum ke yi ko tunani na falsafa

Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar Kaduna Central a majalisa zubi ta 8, ya yi tsokaci kan hoton da ya bazu na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Yan takarar shugaban kasa sun sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya: An nemi Atiku an rasa wajen

An rahoto cewa Bola Tinubu barci ya rika sharba yayin taron da aka shirya don yan takarar shugaban kasa domin tabbatar an yi kamfen lafiya gabanin zaben shugaban kasa.

Shehu Sani da Bola Tinubu
Sanatan PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Zolayi Tinubu Kan Barci Da Aka Ce Ya Yi Ta Sharba Yayin Taro. Hoto: Photo Credit: Shehu Sani, Omoyele Sowore
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehu Sani ya zolayi Tinubu kan barci a wurin taro

Kwamitin zaman lafiya na tsohon shugaban kasa na mulkin soja Janar Abdulsalami Abubakar ne ya shirya taron a ranar Juma'a 20 ga watan Satumba.

A cewar Nigerian Tribune, Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa na Action Alliance ya yi ikirarin cewa dan takarar shugaban kasar na APC barci ya rika yi yayin taron.

Da ya ke martani kan lamarin, Sani ya ce ba kowanne lokaci bane mutane ke barci idan sun rufe ido.

Abin da ke faruwa a baya-baya game da Shehu Sani, Bola Tinubu, APC, PDP, Omoyele Sowore, Zaben 2023

Kara karanta wannan

Uwar Gidan Atiku Ta Bayyana Wani Abin Mamaki Game Da Gwamnatin Obasanjo

Ya ce ta yi wu Tinubu yana wasu addu'o'i ne ko yana tunani na falsafa.

Rubutun da Sani ya yi a Twitter ta ce:

"Lokacin da mutum ya rufe ido ba wai barci ko gyangyadi kadai ya ke ba. Ta yi wu addu'a ne ko tunani na falsafa. Ta yi wu tunanin falsafa Asiwaju ke yi."

Sani yana cikin masu neman takarar kujerar jam'iyyar PDP kuma shine ya samu mafi karancin kuri'a yayin zaben cikin gida na jam'iyyar.

Ga rubutun da ya yi a Twitter a kasa:

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164