Yan Takarar Shugaban Kasa A Nigeria Sun Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Yan Takarar Shugaban Kasa A Nigeria Sun Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

  • Yan takarar shugaban kasa sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabatowar zaben 2023
  • Amma ba'aga Bola Tinubu a wajen sanya hannun ba, harma da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party
  • An dai shirya sanya hannun ne dan magance yawan tashe-tashen hankula da mabiya sukai yi

Abuja - Yan takarar shugaban kasa da zasu fafata a zaben 2023 sun sanya hannu kan shirin zaman lafiya na 2023

Shirin, wanda kwamitin zaman lafiya na kasa ya shirya, a babban dakin taron na otel din Transcorp Hilton dake Abuja. Rahotan Premiun Times

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC wanda bai halarci sanya hannun na farko ba ya halarci wannan tare da mataimakinsa Kashim Shettima da shugaban jam'iyyar Abdullahi Adamu.

Sauran yan takarar da suka halarci sanya hannun akwai Omoyele Sowore na AAC, da Rabi'u Kwankwaso na NNPP, da sauransu.

Kara karanta wannan

Sharɓar Barci Kawai Tinubu Ya Yi Wurin Taron Yan Takarar Shugaban Kasa, Bai Ce Uffan Ba, Sowore

Sai dai kuma, dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da na jam'iyyar LP, Peter Obi, basu halarci sanya hannun ba, amma Ifenayi Okowa ya wakilci ubangidansa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yan Takara
Yan Takarar Shugaban Kasa A Nigeria Sun Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya Hoto: UCG
Asali: UGC

Shugaban kwamitin zaman lafiyan wanda kuma tsohon shugaban Nigeria a mulkin Soji, Abdulsalam Abubakar yake jagoranta, ya ce wannan sanya hannun anyi shine dan tabattar da zaman lafiya lokacin zabe.

Abdulsalam ya yabawa hukumar zabe na yadda ta inganta hanyoyi da kuma dabarun yadda ake zabe, sannan ya ce zaman ba anyi shi bane dan cin mutumci ko kuma yabo ba.

"Ina rokonku duka, ku kiyaye harshenku, ku girmama juna, ba munzo dan yabo ko sukan wani ba, mun zo ne dan ci gaban wannan kasar tamu"
"Mun ga kudirin hukumar zabe wajen bunkasa tare da inganta harkokin zabe a Nigeria"

Kara karanta wannan

Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Kwanta Dama Yayin Da Ake Tsaka Da Yakin Neman Zabe

Abdulsalam yace yaga yadda hukumomin tsaro suma sunyi kokari wajen inta hanyoyi da dabaru wanda suke amfani da su wajen tabbatar da anyi sahihin zabe.

Wani abu da Soware yayi a wajen taron

A yayin da ake tsaka da wannan muhawara an ga Soware na kalubalantar yadda aka shirya zaman, inda yake cewa akwai bukatar ace zaman wajen an shirya shi ne a wasulun sunayen kowa.

"Zaman nan ya kamata ace da harufan sunan kowa akai amfani wajen zaman, wato wasalin kowa yadda zai zauna kenan"

Asali: Legit.ng

Online view pixel