Duk da Umarnin CBN, Bankuna Na Cigaba da Bada Tsofaffin Kudi, 'Yan Kasuwa Sun Koka

Duk da Umarnin CBN, Bankuna Na Cigaba da Bada Tsofaffin Kudi, 'Yan Kasuwa Sun Koka

  • Duk da umarnin da CBN ta bada na umartar bankuna da sakin sabbin kudi a injinan bada kudi, bankunan cikin gari basu daina bawa kwastomomi tsoffin kudi ba
  • Sai dai CBN a ranar Alhamis ta shawarci 'yan kasa da su daina amsar tsoffin kudi daga bankuna cikin gari saboda zasu daina amagani a 31 ga watan Janairu
  • Sai dai, an gano yadda wasu bankuna suke sakin tsoffin kudi a injina bada kudinsu, wanda hakan ya saba dokar CBN kuma akwai yuwuwar za a ci su tara

Duk da umarnin babban bankin Najeriya na zuba sabbin takardun Naira a ATM, bankuna masu tarin yawa a jihohin kasar nan na bayar da tsofaffin kudi.

Babban bankin Najeriya a ranar Alhamis Alhamis ya bukaci ‘yan kasa da su ki karbar tsofaffin kudi daga bankunan ‘yan kasuwa inda ya jaddada cewa zuwa ranar 31 ga watan Janairu tsofaffin kudin za su zama takardun tsire.

Kara karanta wannan

Tof fa: Bankuna sun Ssabawa CBN game da sabbin kudi, suna ta ba mutane tsoffin kudi a ATM

Godwin Emefielee
Duk da Umarnin CBN, Bankuna Na Cigaba da Bada Tsofaffin Kudi, 'Yan Kasuwa Sun Koka. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Babban bankin tun ranar Juma’a, 12 ga watan Janairun 2021 ya bukaci bankuna da su daina ba kwastomomi N1,000, N500 da N200 amma wakilan Legit.ng a jihohi da dama sun gano cewa bankunan ba su bi dokar ba.

Mataimakiyar daraktan ayyuka na CBN, Rekiyat Yusuf, tayi kira ga ‘yan Najeriya da kada su karba Tsofaffin kudi a Lokoja, babban birnin jihar Kogi yayin da take wayar da kan mata da maza ‘yan kasuwa kan sabbin takardun kudaden.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tace duk wani banki da aka kama yana baiwa kwastomomi tsofaffin takardun Naira za a cishi tara.

Sai dai, yayin da Daily Trust ta ziyarci wani injina bada kudi a Kano, ya gano yadda basa bada sabbin kudi.

Bankin Unity na reshen titin Legas, wanda ke da katanga daya da ofishin CBN, baya bada kudi a injinanshi idan karfe 6:00 na yamma tayi.

Kara karanta wannan

Toh fa: CBN ya fadi abin da 'yan Najeriya za su yi idan aka basu tsoffin kudi

Wannan lamarin yayi shige da reshen First Bank da ke kallon ofishin CBN a titi daya.

A Bankin Zenith na titin Zoo, an gano yadda injinan, kusan hudu daga cikinsu suke bada tsoffin kudi.

Kwanturolan CBN rashen Kano, Umar Ibrahim Biu ya ce bankin kolin ba zai yi kasa a guiwa ba wajen cin bankuna tara idan suna karya doka.

A cewarsa, bankin kolin ya umarci bankuna da su guji biyan kudi ta banki ko kada a samu fifiko tsakanin kwastomomi.

A daya daga cikin bankunan jami'ar Legas, wani injin bada kudi yana bada sabbin N1,000 da N500 yayin da sauran ke bada soffin kudi.

Shugaban tawagar CBN na kula da Group C, Owugar Comfort Akinbode, yayin amsa tambayoyin manema labarai a Makurdi, babban birnin jihar Biniwe.

Ta ce:

"Muna bukatar a bi doka a dukkan jihohi da babban birnin tarayya. Shiyasa tawagarmu take nan. Muna so kudin ya isa ga jama'a; shiyasa suke maida hankali a wannan aikin, musamman don duba injinan bada kudinsu, don ganin idan suna bada sabbin kudi."

Kara karanta wannan

Za ku sani: CBN ya fusata, zai yi maganin bakuna yayin da suka ki zuwa daukar sabbin Naira

A cewarta, wajen bada kudin da suka ziyarta sun hada da; Access da bankunan Union da suke bada sabbin kudi.

’Yan Kasuwa sun koka

A zantawa da Legit.ng Hausa tayi da wani ‘Dan kasuwa mai suna Malam Mansur a kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, yace tabbas har yanzu sabbin kudin basu yawaitar da za a ce za a daina karbar tsofaffin ba.

”Tabbas takardun wasu zasu zama na tsire saboda ko ni da kullum mu ke Kasuwa, ba zan ce na rike sabbin kudin sau ashirin ba tun bayan sakinsu da aka yi.
”Yanzu haka kashi 80 na kudin da ake cinikayya da su Duk tsofaffin ne. Ni bai fi kwana hudu da suka gabata ba na taba ganin takardar N1,000. Na ga N500 a wancan makon amma har yanzu ban ga N200 ba.”

- Yace.

Har ila yau, Legit.n Hausa ta zanta da wani mai siyar da kayan marmari a Bata mai suna Mallam Hassan.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Daga ranar 25 ga wata na daina karbar tsoffin Naira, inji dan kasuwa a jihar Arewa

"Toh mun ji cewa babban bankin Najeriya yayi umarnin a daina karbar tsofaffin kudade daga banki. Na je banki yau da safen nan a Zoo Road, amma tsofaffin kudin aka bani kuma haka na karba.
"Zan iya cewa babu adalci matukar aka ce nan da kwanaki goma sha daya tsofaffin kudi sun tashi aiki. Ina da tabbacin cewa mu nan 'yan kasuwa za mu matukar cutuwa. Duk da dai ni ban cika rike tsaba ba, na kan kai POS a saka min a asusun bankina."

- Mallam Hassan yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel