Ijara-Isin, Yankin Jihar Kwara Da Mazauna Yankin Ke Amfani da Kudinsu Ba Irin na Najeriya ba

Ijara-Isin, Yankin Jihar Kwara Da Mazauna Yankin Ke Amfani da Kudinsu Ba Irin na Najeriya ba

  • Yankin Ijara-Isin cikin jihar Kwara, tsakiyar arewacin Najeriya sun dauki wata dabi'ar adana kudi cikin yankin don habaka tattalin arzikin yankin
  • Yankin sun zabi amfani da wani irin kudi da suka kirkira ga mazauna yankin kadai idan suka je kasuwa, wanda Olusin Ijara-Isin ne ya samu dabarar bayan ya ziyarci Amurka a 2021
  • A ganinsu, hakan kamar kariya ne daga sata saboda takardar da suke amfani da ita a matsayin kudin ba za tayi amfani ga wani ba idan ya sata a wajen yankin

Kwara - Yankin Ijara-Isin na jihar Kwara, yanki ne da ke tsakiyar arewacin Najeriya sun dauki wani irin tsarin adana kudi cikin yankin kadai don farfado da tattalin arzikinsu.

Ijara-Isin sun fiddo da nasu 'kudin', wanda aka amince da amfani da shi a cikin yankin, Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Manyan Kura-Kurai Aka Tafka, Rashin Shugabanci Na Kwarai a Kasar Nan na Shekaru 24 ne ya Tsundumata Halin da Muke Ciki

Ijara
Ijara-Isin, Yankin Jihar Kwara Da Mazauna Yankin Ke Amfani da Kudinsu Ba Irin na Najeriya ba. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Manajan daraktan kungiyar tattalin arzikin Ijara-Isin, Alo Oluwafemi, yayi jawabi game da dalilin da yasa suka fitar da nasu kudin, wanda suke kira kudi, wanda mazauna yankin Ijara-Isin ke amfani da shi idan su ka je kasuwanni.

Oluwafemi ya ce Olusin na Ijara-Isin, Oba Ajibols Ademola Julius, ya samu dabarar ne yayin da yayi tafiya birnin Amurka a 2021, jaridar Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya labarta yadda basaraken ya lura da duk lokacin da ya bada kyautar kudi ko aiki, mazauna yankin sun zabi adana kudin a asusun bankinsu ko amfani da shi wajen garin Ijara-Isin wanda hakan baya taimakon yankin, saboda haka ne yayi tunanin adana kudi a cikin yankin.

A matsayin ma'aikacin yankin, Akinleye Tolulope, ya ce dabarar hakan ta samo asali ne don habaka tattalin arzikin yankin.

Ya kara da cewa ana biyan mazauna yankin da 'kudin' don karfafa mazaunan daga amfani da wani kudi, sai dai kashewa a yankin don taimakawa wajen cigabansu.

Kara karanta wannan

Babbar Nasara: Luguden Bama-Bamai Ya Sheke Daruruwan Yan Bindiga a Jihar Arewa 1

Jami'in da ke da alhakin amsar kudin kungiyar Ijara-Isin, Mukaila Abdulrahman, ya bayyana yadda ake amfani da kudin.

Abdulrahman ya ce dole ne rattaba hannu da buga hatimi don taimakawa mutum kashewa, inda ya kara da cewa, idan mazauna yankin na son canza takardar zuwa kudi, suna da damar yin hakan.

Oluwafemi ya kara da cewa, idan 'yan kasuwa suka amsa kudin, suna kai shi ofishin inda aka adana kudaden a asusunsu daga bisani a mayar da kudi don bawa 'yan kasuwa damar sake amfani da shi.

Wani 'dan kasuwa, Babalols Omolara, ya ce kudin da suke amfani da shi ya taimakawa yankin kuma hakan kariya ne daga sata duba da bai da amfani da duk wanda ya sata daga garesu.

Haka zalika, wani 'dan kasuwa, Oluwabukola Ojo, ya ce suna amsar kudi daga 'yan wajen yankin wadanda ke son siyan kaya.

Daliba ta kafa kasuwanci da kudin makarantar ta

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Kama Jarumin da ya Caka wa Makwabcinsa Wuka a Kirji kan N1,000

A wani labari na daban, wata budurwa ta sanar da yadda ta kirkiri kasuwancinta yayin da ta ke makarantar jami'a.

Tace tana kwance a gadonta na makaranta dabarar ta fado mata kuma ta debi kudin makarantarta ta aiwatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel