Baiwa Daga Allah: Bidiyon Yarinya Makauniya Tana Rangada Kitso da daura Gwagwaro

Baiwa Daga Allah: Bidiyon Yarinya Makauniya Tana Rangada Kitso da daura Gwagwaro

  • An ga wata makauniyar yarinya 'yar Najeriya mai matukar fasaha a wani bidiyo tana kitsa kan wata gwanin ban sha'awa
  • Yarinyar wacce ake kira Victoria har yanzu daliba ce, kuma tana kitsa kan wata daliba abokiyar karatunta a makaranta
  • Baya ga fasahar iya kitsa gashi, Victoria na iya daura kallabi sannan ta bayyana burinta da koyan kwalliya

Wata yarinya makauniya 'yar Najeriya da ke da fasahar kitsa gashi tayi yawo a yanar gizo. An ga yarinyar mai suna Victoria a wani bidiyo da Michael Thompson Showunmi ya wallafa a Twitter tana bayyana fasaha da baiwa.

Victoria
Baiwa Daga Allah: Bidiyon Yarinya Makauniya Tana Rangada Kitso da daura Gwagwaro. Hoto daga Twitter/Cycogreat.
Asali: Twitter

Duk da makantarta, Victoria na iya kitsa gashin abokiyar karatunta a salo na kwarewa.

Victoria cikin sigar kwarewa ta kama gashin wata daliba da mataji gami da kitsawa kamar tana ganin komai ta ke yi.

Kara karanta wannan

Ina Jin Yaruka 3: Budurwa Yar Abuja Da ke Kwasan Albashi Rabin Miliyan Tana Neman Mijin Aure, Ta Fadi Irin Wanda Take So

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Baya da iya kitsa gashi da tayi, Victoria ta iya daurin kallabi, abun da ke da matukar wahala ga wadanda ke iya gani.

Haka zalika, ta bayyana yadda take son koyan kwalliya. A cewarta, babu abun da ba-zata iya ba. Wani tsokaci karkashin bidiyon Victoria ya bayyana:

"Victoria, wata makauniyar yarinyar da ke kitsa gashi, tana kitsa gashin wata abokiyar karatunta... ba a nan ta tsaya ba, ta iya daurin kallabi. Sannan tana so ta koyi kwalli.

A cewarta:

"Idan har an koya min, babu abun da ba zan iya ba"

Martanin jama'a

@Brainmartin29 ya ce:

"Ubangiji da girma yake."

@Abiodun756 yayi tsokaci:

"Babban abun al'ajabi."

@Sunrule3 yayi tsokaci:

"Ki cigaba da hakan yana da kyau!!"

@makaveli18790 ya ce:

"Wannan abu yayi kyan gani."

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Ta Auri Mai Nakasu Bayan Ta Rabu Da Attajirin Saurayinta

Sau da yawa Ubangiji kan ba nakasassu baiwar da bai ba wa mai cikakkiyar halitta ba, hakan kan ba jama'a mamaki duk da dai ba abun mamaki bane idan aka duba taskar Allah.

Kun yi abun kunya, Fasto ya yi wa 'yan coci tatas kan bada sadakar N100, N20

A wani labari na daban, wani fasto yayi wa jama'ar cocinsa wankin babban bargo kan bayar da sadakar N100 da N20.

Faston Najeriyan ya bayyana cewa, hatta man fetur da ya ke amfani da shi wurin tada janareton wa'azi lita 20 ya zubawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel